Koma Labarai
Shari'a

Ƙungiyoyin Muslunci a Kano sun buƙaci a gurfanar da Malam Lawan Triumph a kotu kan zargin ɓatanci ga Ma'aiki.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Ƙungiyoyin Muslunci a Kano sun buƙaci a gurfanar da Malam Lawan Triumph a kotu kan zargin ɓatanci ga Ma'aiki.

Babbar Kotun jaha mai lamba 2 karkashin jagorancin mai shari'a Yusuf Ubale Muhammad, ta sanya ranar 23 ga wannan watan don ci gaba da sauraron shari'ar nan wadda ƙungiyoyin muslinci suka shigar, suna ƙarar gwamnatin Kano da Kwamishinan yansanda da na Shari'a.

Masu ƙarar dai suna roƙon kotun da ta sanya a gurfanar da Mallam Lawan Abubakar Triump, akan zargin sa da ɓatanci ga fiyayyen halitta.

A zaman kotun na yau Alhamis 4 ga Yuni, 2026, masu ƙarar sun gabata a gaban kotun, sai dai ɓangaren gwamnati basu bayar da martaninsu a rubuce ba, a nan ne lauyoyin gwamnatin suka roƙi kotun ta basu wata rana don yin martani.

Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma'il ya ruwaito cewa, kotun ta sanya ranar 23 ga wannan watan na Yuni, 2026, an kuma gargaɗi lauyoyi da su gabatar da martanin idan kuma ba haka ba za, a saurari rokon masu ƙara.

Ready to PlayDala FM88.5 FM