Koma Labarai
Labarai

Hukumar Hisbah ta sanar da makon auren gatan da gwamnatin Kano za ta yi a jihar.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Hukumar Hisbah ta sanar da makon auren gatan da gwamnatin Kano za ta yi a jihar.

Hukumar Hisbah ta jihar Kano, ta ce za a shiga makon auren gata da gwamnatin Kano za ta yi, daga ranar Litinin 3 ga watan Agusta, 2026.

Mataimakin Babban Kwamandan hukumar, Dr. Mujahideen Aminudden Abubakar, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya aiko wa Dala FM, a ranar Alhamis 30 ga Yuli, 2026.

Ya ce ana buƙatar duk waɗanda suka tabbatar da cewa an tantance su dangane da auren gatan da za a yi musu, su je Kananan Hukumomin su ɗauke da katin da aka tantance su da "Certificate" ɗin da aka basu, domin karɓar Shadda da Hula, da Atamfa, da Hijabi.

A cewar sa, ba za a basu waɗannan kayayyaki ba har sai sun nuna katin tantancewar tasu, yana mai cewa sauran mutanen na cikin birnin Kano, za su je Hedikwatar Hukumar Hisbah ta jihar Kano, domin su karɓi nasu kayayyakin da misalin ƙarfe 10:00 na safe.

Dr. Mujahideen ya kuma ce, za a ɗaura wa mutanen auren ne a ranar 7 ga watan Agustan 2026, amma na ƙananan hukumomin karkara, su kuwa na hedikwatar hukumar za a sanar da ranar da za a ɗaura musu aure gatan na gwamnatin jihar Kano.

"Ya ƙara da cewa waɗanda za su ci gajiyar auren gatan, za su je fadar masarautun yankin su ne a ranar daura auren, da suka haɗar da na yankin Rano, Ƙaraye, Gaya, wanda a nan ne dukka za a ɗaura musu auren," in ji shi.

Ya kuma ce gwamnatin jihar Kano za ta shirya wa masu cin gajiyar auren gatan walima a ranar 8 ga watan Agusta, inda za a gwangwaje a gidan gwamnatin jihar, daga bisani kuma a rarraba musu gidajen su.

Ready to PlayDala FM88.5 FM