Majalisa ta buƙaci gwamnatin Kano ta ƙara asibitocin kula da masu taɓin Ƙwaƙwalwa a jihar
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Majalisar dokokin jihar Kano ta buƙaci gwamnatin jihar da ta samar da ƙarin asibitocin masu fama da larurar ƙwaƙwalwa a ɓangarori uku na jihar Kano.
A yayin zaman majalisar dokokin na yau Litinin, ƙarƙashin jagorancin shugaban ta Jibril Isma'il Falgore, ɗan majalisa mai wakiltar ƙananan hukumomin Bagwai da Shanono, Ali Lawan Alhassan Kiyawa, ne ya gabatar da ƙudirin.
Ali Lawan ya ce asibiti guda biyu ne kawai aka dogara da su a jihar Kano, kuma mafi akasarin marasa lafiyar da ake da su ƴan ƙwaya ne, a don haka akwai buƙatar ƙarin wasu asibitin.
Wakilinmu Sunusi Shu'aibu Musa ya ruwaito cewa, ɗan majalisar ya kuma ce da yawa daga cikin manyan laifukan da ake aikatawa na da alaƙa da matsalar ƙwaƙwalwa.



