Rundunar Ƴan Sanda ta gargaɗi masu hawa Takalmin taya suna tsere a titunan Kano
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta gargaɗi masu hawa Takalmin taya suna tsere a kan tituna a cikin garin Kano, da su daina domin gujewa abinda ka je ya dawo.
Tashar Dala FM Kano ta ruwaito cewa jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya yi wannan gargaɗi a shafin sa na Facebook, a ranar Juma'a 5 ga Yuni, 2026.
Rundunar ƴan sandan ta kuma ce matuƙar masu hawa Takalmin tayar a kan titunan suna tsere ba su daina ba, babu makawa aiki zai biyo ta kan su.



