Bayan mutuwar Tumaki da Awaki, yanzu mutane sun fara rasuwa a ramin "I love you" da ke Ɗorawar dillalai a Kano - Mazauna yankin
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Al'ummar unguwar Ɗorawar dillalai da ke ƙaramar hukumar Ungogo a Kano, sun koka bisa yadda wani kududdufi ya ciko, kuma ciyawa da Kainuwa suka fito a saman shi, inda ya saje da ƙasa yana cin rayukan Mutane a yankin.
Wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya zanta da wani mazaunin yankin mai suna Rudwan Muhammad, wanda ya bayyana cewar kududdufin ya cika sai ciyawa da kainuwa suka fito a saman sa hakan ya sanya mutane suke fadawa.
Ya kuma ce yanzu haka ta kai ga cewa ba a yin wata ɗaya sai an rasa rai sakamakon fadawar da mutane suke yi a cikin Kududdufin.
Ya kuma bayyana cewar sun yi iya bakin ƙoƙarin su amma sun gaza cike ramin, a don haka su ke neman tallafin mahukunta a kan al'amarin da su kai musu ɗauki wajen cike Kududdufin.



