Ba za mu lamunci duk wani nau’in ta’addanci ba a Kano - Hukumomin tsaro

Haɗakar hukumomin tsaro a Kano sun tabbatar da cewa daga yanzu ba za su lamunci duk wani nau’in ta’addanci, da ɓata gari ko ayyukan masu garkuwa da mutane a faɗin jihar ba, domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma da kuma tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa.
Kwamishinan ’Yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da aka gudanar a harabar gidan gwamnatin jihar Kano, bayan kammala zaman majalisar tsaro da gwamnan jihar Injiniya Abba Kabir Yusuf ya jagoranta, domin duba halin tsaro da kuma nemo hanyoyin daƙile matsalolin rashin tsaron da suka fara bayyana a wasu yankuna na jihar a ƴan kwanakin nan.
CP Bakori ya ce zaman majalisar tsaron na ranar Talata, an tattaro shugabannin hukumomin tsaro daban-daban da suka haɗa da rundunar ’yan sanda, da DSS, da Civil Defence, da kuma sojoji da sauran jami’an tsaro, domin yin nazari kan matsalolin da suka shafi tsaro da kuma tsara sabbin dabarun aiki na bai ɗaya.
A cewarsa, hukumomin tsaron sun cimma matsaya kan ƙarfafa sintiri a muhimman wurare, ƙara yawan jami’an tsaro a yankunan da ake ganin suna da matsala, da kuma gudanar da ayyukan leƙen asiri domin gano masu hannu a aikata laifuka kafin su aiwatar da muggan manufofinsu.
CP Bakori ya kuma jaddada cewa duk wanda aka samu da hannu wajen tayar da zaune tsaye, da garkuwa da mutane, da fashi da makami ko sauran laifuffuka zai fuskanci hukunci, kamar yadda doka ta tanada, yana mai cewa babu wanda za a ɗaga wa ƙafa ko a bari ya ci gaba da barazana ga zaman lafiyar jihar Kano.



