Kotun Koli ta bai wa David Mark nasara a shari’ar sa da Nafi’u Bala
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Kotun Koli ta Najeriya ta yanke hukunci a shari’ar da ke tsakanin David Mark da Nafi’u Bala, inda ta bai wa David Mark nasara a matsayin halastaccen shugaban jam’iyyar ADC a ƙasar.
A ranar Alhamis 30 ga watan Afrilu, 2026, ne dai kotun ƙolin ta yanke hukuncin, da ya gudana a babban birnin tarayya Abuja.
Kotun ta kuma yi watsi da wasu muhawara da aka gabatar a gaban ta, tana mai cewa ba su da muhimmanci ga shari’ar kuma ba su da tasiri wajen yanke hukunci.
Wannan hukunci na nuni da kawo ƙarshen takaddamar da ta dade tana jan hankalin jama’a a tsakanin ɓangarorin biyu, ko da ike kotun ta ce a koma babbar kotun tarayya domin ci gaba da shari'ar da aka faro a baya.



