Rashin wutar lantarki, ruwan sha, Asibiti, da Hanya na damun yankin mu - Mazauna Mushuni a Kano

Al'ummar garin Mushuni da ke ƙaramar hukumar Ungogo a Kano, sun koka tare da neman ɗaukin mahukunta kan yadda matsalar rashin kyan hanya, da wutar lantarki da ruwa, da kuma asibiti, al'amarin da suka ce na damun su.
Mazauna yankin na Mushuni dai da ke ƙaramar hukumar Ungogo, sun ce sun haura shekara da shekaru suna fama da ƙalubalen ƙarancin al'amuran more rayuwa, al'amarin da yake zama alaƙaƙai a gare su.
Usman Musa guda ne daga cikin mazauna garin Mushuni, ya ce suna iya ƙoƙarin su a ƙungiyance domin ganin mahukunta sun kawo musu ɗauki dangane da ƙalubalen da suke fuskanta na rashin kyan hanya, da wutar lantarki, da ruwan sha, da kuma rashin asibiti.
Ya ce kawo yanzu ba a magance musu matsalolin da suke damunsu a yankin nasu ba, duk kuwa da yadda suke zaɓen shugabanni idan lokaci ya yi.
A cewar wani dattijo mazaunin yankin Mushuni da ke ƙarƙashin dagacin Kakurum, ya haura shekaru sittin ba tare da ya ga wani babban aiki na ku zo mu gani daga ɓangaren mahukunta a yankin nasu ba.
Dattijon ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar Kano, da shugabancin ƙaramar hukumar su na ƙaramar hukumar Ungogo, da su kai musu ɗauki wajen magance musu ƙalubalen da ke damun su domin samun wani sauƙi.
Da yake nasa jawabin Nazifi Abdullahi, wakilin mai unguwar yankin Mushuni da ke ƙarƙashin dagacin Kakurum a karamar hukumar Ungogo, ya ce sun daɗe da miƙa korafe-korafen al'ummar yankin zuwa gurin mahukunta.
Dala FM Kano ta ruwaito cewa Nazifi ya kuma ce zuwa yanzu an magance wasu matsalolin, amma dai suna ci gaba da bibiya don ganin an magance sauran ƙalubalen da ake fuskanta a unguwar tasu.


