Direbobin baburan adai-daita sahu ku daina ɗaukar mata a gefen ku, kasancewar yin hakan haramun ne - Hukumar Shari'a a Kano.

Hukumar Shari'a ta jihar Kano, ta buƙaci direbobin baburan adai-daita sahu, da su daina ɗaukar mata a gefen hagu da daman su, da ake kira da "Attachment" kasancewar yin hakan haramun ne a mahanga ta addinin Musulunci, bisa cuɗanyar da ake yi da matan.
Kwamishinan na biyu a hukumar Shari'ar addinin Musulunci a jihar nan Sheikh Ali Ɗanabba ne ya bayyana hakan yayin da gamayyar ƙungiyoyin shugabannin direbobin baburan adai-daita sahu ta Voice of trickle owners and riders, (VOTORA) suka amsa gayyatar da hukumar ta yi musu, a ranar Alhamis 30 ga Yuli, 2026.
A yayin ganawar da ɓangarorin biyu suka yi a hukumar shari'ar, sun tattauna mahimman batutuwa da za su ƙara kawo tsari da tsafta a sana'ar adai-daita sahu, a faɗin jihar Kano.
Sheikh Ali Ɗanabba ya kuma ce, sun gayyaci shugabannin gamayyar ƙungiyoyin masu baburan adai-daita sahun ne, domin ƙulla alaƙa ta yadda za su taimaka wajen magance abubuwan da suka damu al'ummar jihar nan, ciki har da sace-sacen yara da kuma yaƙi da sha da dillancin miyagun ƙwayoyi, da ƙara kawo tsafta a harkar tuƙa adai-daita sahu da sauran su.
Dala FM Kano ta ruwaito cewa, Malamin ya kuma buƙaci direbobin baburan adai-daita sahu, da su daina ɗaukar mata a gefen su ɓangaren hagu da dama, da ake kira da "Attachment" kasancewar yin hakan haramun ne a mahanga ta addinin Musulunci, bisa cuɗanyar da ake yi da matan.
Da yake nasa jawabin, shugaban Ƙungiyar Gamayyar Ƙungiyoyin baburan adai-daita sahu, ta Voice of trickle owners and riders, (VOTORA) Nazifi BK Gidan kuɗi, ya ce a shirye suke wajen bayar da dukkan haɗin kan da ya dace ta ɓangarori daban-daban, domin ganin an samu ci gaba a faɗin jihar.



