Koma Labarai
Labarai

KAROTA ta nemi gwamnati da ta shiga tsakani kan rikicin da ake samu tsakanin su da wasu jami'an soji a Kano

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
KAROTA ta nemi gwamnati da ta shiga tsakani kan rikicin da ake samu tsakanin su da wasu jami'an soji a Kano

Shugaban Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano (KAROTA), Injiniya Faisal Mahmud Kabir, ya bayyana damuwarsa kan yawaitar samun saɓani tsakanin jami'an KAROTA da wasu jami'an rundunar sojin Najeriya yayin gudanar da ayyukan kula da zirga-zirgar ababen hawa a sassan jihar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Jami'in Hulɗa da Jama'a na hukumar, Abubakar Ibrahim Sharada, ya fitar a madadin shugaban hukumar, Injiniya Faisal Mahmud Kabir.

Sanarwar ta ce, doka ta bai wa KAROTA ikon tsara zirga-zirgar ababen hawa, tabbatar da kiyaye dokokin hanya da kuma kare lafiyar masu amfani da hanya. Sai dai hukumar ta nuna damuwa cewa wasu jami'an soja kan ƙi bin dokokin hanya da umarnin da jami'an KAROTA ke bayarwa yayin gudanar da aikinsu.

Shugaban hukumar ya kuma ce duk da girmamawar da KAROTA ke yi wa rundunar sojin Najeriya, bin dokokin hanya wajibi ne ga kowa da kowace hukuma ba tare da wani banbanci ba.

Saboda haka, shugaban KAROTA ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano, shugabannin rundunar soji da sauran masu ruwa da tsaki da su shiga tsakani domin ƙarfafa haɗin kai da fahimtar juna tsakanin hukumomin biyu. Ya ce hakan zai taimaka wajen kauce wa irin waɗannan matsaloli a nan gaba, tare da inganta gudanar da ayyuka da tabbatar da tsari da aminci a hanyoyin jihar Kano.

Ready to PlayDala FM88.5 FM