Koma Labarai
Labarai

Gwamnatin Kano za ta samar da rijiyoyin burtsatse masu sola 166 don magance karancin ruwa a jihar

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Gwamnatin Kano za ta samar da rijiyoyin burtsatse masu sola 166 don magance karancin ruwa a jihar

Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya amince da samar da rijiyoyin burtsatse guda 166 masu amfani da hasken rana a sassa daban-daban na jihar domin magance matsalar karancin ruwa da kuma inganta samar da tsaftataccen ruwan sha ga al’umma.

Muƙaddashin kwamishinan albarkatun ruwa na jihar, Dakta Dahir Muhammad Hashim, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, inda ya ce shirin na daga cikin matakan gaggawa da gwamnatin jihar ke ɗauka domin rage ƙarancin ruwa a yankunan da abin ya shafa.

Ya kuma ce ana sa ran rijiyoyin za su samar da kimanin lita miliyan 4.15 na ruwa a kullum, tare da amfani ga kusan mutane 830,000 a faɗin jihar.

A cewarsa, "Kowace rijiyar daga cikin guda 166 za ta rika samar da kimanin lita 25,000 na ruwa a rana tare da yi wa kusan mutum 5,000 hidima," in ji Ɗahir.

Hashim ya bayyana cewa wannan shi ne mataki na farko na aikin, yana mai cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da amincewa da ƙarin rijiyoyi domin faɗaɗa aikin zuwa wasu ƙarin al’ummomi a jihar.

Ya kuma bayyana cewa an fara aikin gyaran cibiyoyin tace ruwa na Tamburawa da Challawa, bayan gwamnatin jihar ta amince tare da bayar da kwangilar ayyukan.

Ready to PlayDala FM88.5 FM