Matasa ku daina yarda ana amfani da ku wajen tayar da tarzoma a Kano - Human Rights

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Center for Human Rights and Charity Development initiatives, ta buƙaci matasa da su guji yarda wasu su rinƙa amfani da su wajen tayar da tarzoma, da rikicin daba, da shaye-shaye, a yayin bikin Babbar Sallar nan da ake ciki.
Babban Daraktan ƙungiyar a Najeriya, Kwamared Dr. Auwal Jibril Maifada, ne ya bayyana hakan a yayin zantawar sa da Dala FM Kano a ranar Alhamis 28 ga Mayu, 2026, a wani ɓangare na Barka da Babbar Sallah, da ya yi wa al'ummar Musulmi.
Ya kuma ja hankalin matasan da su guji yin duk abinda ka iya kawo rashin zaman lafiya a cikin al'umma, "matasa ku tuna cewa ku ne ginshiƙin cigaban ƙasa don haka ya kamata ku kasance masu nagarta, biyayya da bin doka, in ji Dr Auwal.”
Har ila yau, Maifada ya kuma yi kia ga iyaye da su sanya ido sosai a kan tarbiyyar ƴaƴansu, musamman ma a wannan lokuta na bukukuwan Babbar Sallah, domin kare su daga faɗawa cikin munanan ɗabi'u da abubuwan da ka iya jefa rayuwar su cikin haɗari.
Dr. Auwal Maifada ya kuma taya ɗaukacin al'ummar musulmin duniya murnar Babbar Sallah, inda ya kuma yi addu'ar Allah ya karɓi ibadun mu, ya sanya albarka a cikin waɗannan ranakun sallar, ya ƙare ƙasar nan daga dukkan fitintinu, tare da ɗorewar zaman lafiya da haɗin kai a tsakanin al'ummar Najeriya.



