Majalisar Dokokin Kano ta amince da ƙudurorin kafa kwalejojin kimiyyar lafiya huɗu a jihar.

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da ƙudurorin kafa kwalejojin kimiyyar lafiya huɗu da kuma ƙudirin ƙarin kasafin kuɗin jihar na shekarar 2026.
Amincewar ta zo ne a zaman majalisar da ta tattauna ƙudurorin a ranar Talata 20 ga Octoba, 2026, waɗanda suka shafi bunƙasa harkokin ilimin kimiyyar lafiya da kuma ƙarin kasafin kuɗin jihar.
Ƙudurorin kafa kwalejojin sun haɗa da na Rogo, Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kano, ta Bebeji, da kuma Kwalejin Kimiyyar Lafiyar Jama'a ta Kano.
Jibril Ismail Falgore, dake wakiltar ƙaramar Rogo kana Kakakin majalisar ta Goma, ya bayyana kwalejin lafiya da za a samar a Rogo za ta samar da cigaba tare da bunƙasa tattalin arziki.
Wakilinmu na majalisar Sunusi Shuaib Musa ya ruwaito cewa majalisar ta amince da ƙudirin ƙarin kasafin kuɗi da gyaran kasafin kuɗin jihar na shekarar 2026.



