Kotu ta aikewa Malam Lawan Triumph sammaci kan zargin kalaman tunzurawa al'umma a Kano.
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Ƙofar Kudu a jihar Kano, ta aikewa Malam Lawan Triumph sammaci domin ya bayyana a gabanta.
Kotun, ƙarƙashin jagorancin Alƙali Ibrahim Sarki Yola, ta bayar da sammacin ne bayan ƙarar da wasu ƙungiyoyin addinin Musulunci suka shigar a gaban ta.
Ƙungiyoyin, ƙarƙashin jagorancin Muhammad Al-Bakary Mika'il, suna zargin Malam Lawan Triumph da yin kalaman da ka iya tunzura al’umma.
Ana sa ran wanda ake ƙara zai bayyana a gaban kotun domin amsa ƙarar da aka shigar a kansa.



