Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta buƙaci gwamnatin Kano ta ɗaga likkafar asibitin garin Ja'en

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Universal Declaration of Human Rights ta jihar Kano, ta buƙaci gwamnatin jihar Kano da ta faɗaɗa Asibitin sha ka tafi na garin Ja'en da ke ƙaramar hukumar Gwale, domin ƙara inganta lafiyar al'ummar yankin da kewaye.
Daraktan ƙungiyar a matakin jihar Kano, Kwamared Umar Sani Galadanci, ne ya bayyana hakan ta cikin wani saƙo da ya aikowa Dala FM Kano, a ranar Lahadi 21 ga watan Yuni, 2026.
Ya ce sun lura da cewa al'umomi da dama na yankin Ja'en, da maƙotan su, ne ke zuwa asibitin domin duba lafiyar su, amma asibitin ya yi musu kaɗan bisa yadda yake a yanzu.
A cewar sa, "Duba da yadda asibitin yake samun jama'a da dama, idan mutum ya je neman lafiya ma zai iya fitowa da wata cutar mai-makon samun lafiya saboda cikowar mutane bisa kaɗan da asibitin ya yi, in ji Galadanci.”
Kwamared Umar Galadanci ya kuma ce, sun lura baya ga yadda al'ummar Ja'en suke zuwa asibitin, akwai kuma maƙotansu da suma su ke zuwa, irin na yankin Bubbugaje, Sharaɗa, Ja'en Shago tara, Jilawa, Sabon Titi, da sauran gurare masu yawa.
A saboda haka, "Mu ke kira ga gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, da ƙungiyoyin kula da lafiya, a taimaka a faɗaɗa asibitin wajen sayen gidajen bayan asibitin, domin ƙara inganta lafiyar al'ummar yankin da ma kewaye, in ji Umar.”



