Koma Labarai
Tsaro

Wata uwargida ta ƙona mijinsu, da kishiyarta, da yara guda biyu a Kano.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Wata uwargida ta ƙona mijinsu, da kishiyarta, da yara guda biyu a Kano.

Rundunar ƴan sandan jihar Kano, ta cafke wata mata mai suna Maryam Usman, mai shekaru 82, mazauniyar Mangwarori Mariri a Kano, bisa zargin ta da ƙona mijinsu, da kishiyar ta Fiddausi Saminu, da ƴaƴanta guda biyu saboda zafin kishi.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kano CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya aikowa Dala FM Kano, a ranar Laraba 13 ga Mayu, 2026.

Ya ce rundunar ta samu kiran gaggawa ne kan yadda matar mai suna Maryam Usman, ta cinnawa ɗakin kishiryar ta wuta, lamarin da ya yi sanadiyyar ƙonewar sassan jikin mijin su, da kishiryar ta, da kuma ƴaƴan ta guda biyu, a ranar 12 Mayu, 2026.

A cewar sa, "Bayan faruwar lamarin ne jami'an mu suka garzaya da mutanen hudu zuwa Asibitin Sir. Sanusi, inda aka kwantar da su domin basu agajin gaggawa," in ji shi.

CSP Abdullahi Kiyawa, ya kuma ce yanzu haka tuni Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano CP Ibrahim Adamu Bakori, ya ba da umarni a mayar da matar da ake zargin zuwa ga babban sashin binciken manyan laifuka da ke Bompai a Kano, domin ci gaba da bincike.

A cewar sa, tambayoyin da aka yi wa matar ma farko, ta tabbatar da cewa ita ce ta zuba fetur tare da kunna musu wutar har suka samu ƙuna a sassan jikin su.

Ya ƙara da cewa, da zarar an kammala bincike a kan matar za a gurfanar da ita a gaban kotu domin girbar abinda ta shuka.

Rundunar ƴan sandan ta kuma yi kira ga al'umma da su daina ɗaukar doka a hannu, tana mai cewar duk wanda ya ga an yi masa wani abu na ba dai-dai ba to ya je ofishin ta mafi kusa ya shigar da ƙorafinsa.

Ready to PlayDala FM88.5 FM