Manyan Labarai
Kowa ya ajiye mukamin sa Nan da kwanaki hudu – Ganduje

Gwamnatin Kano karkashin jagorancin Dakta Abdullahi Umar Ganduje tace dukkanin masu rike da mukaman siyasa, kama daga kwamishinoni da S.A, S.A da sauran duk wasu masu rike da mukaman siyasa a gwamnatin Ganduje, da su a jiye aikin su Nan da kwanaki hudu.
Cikin wata sanarwa da gwamnatin ta fitar tace tana sanar da duk Wani me rike da mukamin siyasa cewa, mukaman su gaba daya wa’adin su zai kare ne a ranar 29 ga wannan wata na Mayu.
A ranar 29 ga wannan wata ne dai gwamnatin APC za ta Mika Mulki ga Gwamnatin NNPP, karkashin jagorancin zababben gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf.

Manyan Labarai
DSS sun kama Emefele bayan dakatar dashi daga Gwamnan banki

Rahotanni na cewa jami’an tsaro na farin kaya DSS sunyi awon gaba da Godwin Emefele, sa’a guda bayan Shugaban kasa Asuwaju Bola Ahmad Tinubu ya dakatar dashi daga Gwamnan babban banki.
Tun abaya dai an zargi Emefele da hannu wajen gurgunta tattalin arzikin kasa, baya ga zargin sa, da hannu wajen tabarbarewar tsaro.

Manyan Labarai
Da na hadu da kwankwaso da sai na mare shi – Ganduje

Tsohon Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje yace da sun hadu da kwankwaso da akwai yiyuwar ya mare shi, a fadar shugaban kasa.
Tsohon Gwamnan ya bayyana Hakan ne yayin wata ganawa da gidan television na channels, yayin da yake martani Kan ganawar shugaban kasa Asuwaju Bola Ahmad Tinubu da Kuma jagoran jam’iyyar NNPP Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a yammacin wannan juma’a.
” Nasan yana gidan Amma bamu hadu ba, da mun hadu akwai yiyuwar na kwada masa Mari” inji Ganduje.
Idan za’a iya tunawa dai kwanakin baya shugaban kasa Asuwaju Bola Ahmad Tinubu yayi wata ganawa da kwankwaso, lamarin da aka jiyo tsohon Gwamnan na korafi cewa ba’a Yi musu adalchi ba, Koda dai a wancan lokaci, Ganduje ya musanta, ta bakin tsohon kwamishinan yada labarai Muhammad Garba, inda yace ba muryar Ganduje bace.
Wannan dai na zuwa ne a Gabar da gwamnatin Kano ke cigaba da rushe wuraren da tayi zargin gwamnatin baya ta Abdullahi Umar Ganduje ta cefanar ba bisa ka’ida ba.

Manyan Labarai
Gargadin Gwamnatin Kano Kan masu kaya a wuraren gwamnati

Gwamnatin jihar Kano ta gargadi dukkanin masu kaya a wuraren da tayi zargin gwamnatin baya ta cefanar ba bisa ka’ida ba, dasu kwashe kayan su cikin gaggawa.
Cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin Dakta Abdullahi Baffa Bichi ta fitar ta bayyana cewa, dukkanin masu kaya a shagunan da aka gina a jiki ko cikin makarantu, Maƙabartu, Asibitoci, Masallatai, gefen badala, Filayen ma’aikatu, Filayen wasanni da sauran wuraren shakatawa mallakin gwamnati da cewa suyi gaggawar kwashe dukkanin kayan su dake cikin shagunan da aka gina a waƴannan gurare ba tare da ɓata lokaci ba.

-
Nishadi4 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Manyan Labarai3 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai3 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi4 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai3 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya1 year ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Nishadi4 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
-
Manyan Labarai3 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano