Connect with us

Labarai

Tun bayan hawan Buhari abubuwa suka tabarbare – Al-Mustapha

Published

on

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Action Alliance (AA), Manjo Hamza Al-Mustapha (mai ritaya), ya ce, yana son ya zama shugaban kasa a shekarar 2023, domin sake mayar da kasar tsarin gaskiya.

Al-Mustapa, ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a lokacin da ya fito a matsayin bako a gidan talabijin na Channels.

Tsohon dogarin tsaron marigayi Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha (mai ritaya), ya tabbatar da cewa, alkalumma daban-daban sun nuna cewa, kasar nan na ci gaba da rugujewa, tun bayan hawan gwamnatin Muhammadu Buhari ya karbi mulki a shekarar 2015.

Al-Mustapha ya yi ikirarin cewa, kishinsa da kaunarsa ga Najeriya ne ya sa ya sake tsayawa takarar shugaban kasa a 2023, bayan wasu kiraye-kirayen da ‘yan Najeriya suka yi da ya tsaya takarar shugaban kasa.

Al-Mustapha, ya ce, “Bai shiga takarar shugaban kasa don neman kudi ba kamar yadda wasu za su yi tunani”.

Ya ce: “Na yanke shawarar a wannan karon na amsa kiran al’umma daga cikin dattawan Najeriya da matasa daga Arewa zuwa Kudu da kuma wasu makusanta da yawa da na yi aiki da su, na amince da wannan kira na in tsaya takara.

Labarai

Rahoto: Mu nisanci abinda Allah Ya hana domin samun saukin rayuwa – Limamin Tukuntawa

Published

on

Limamin masallacin juma’a na Masjidul Kuba da ke unguwar Tukuntawa a jihar Kano, Malam Ahmad Ali, ya ce, al’umma su duba tsakanin su da Allah tare da nisantar abinda ya hana, domin saukin tsadar rayuwa.

Malam Ahmad Ali, ya bayyana hakan ne, yayin da yake yiwa wakilin mu na ‘yan Zazu,  Ibrahim Abdullahi Soron Dinki, Karin bayani dangane da abinda hudubar da ya gabatar ta kunsa.

Akwai cikakken bayanin hudubar a muryar da ke kasa.

 

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Rubutu na da muhimmanci a mu’amalar bashi – Limamin Bompai

Published

on

Limamin masallacin juma’a na Shelkwatar rundunar ‘yan sandan jihar Kano da ke unguwar Bompai, SP Abdulkadir Haruna, ya ce, akwai bukatar mu rinka gudanar da mu’amalar bashi yadda addinin musulunci.

SP Abdulkadir Haruna, yana bayyana hakan, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Abba Isah Muhammad, bayar idar da Sallar Juma’a.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Matashi ya yi yunkurin cinye tabar Wiwin da aka kama shi da ita a hanyar kotu

Published

on

Ana zargin wani matashi ya yi yunkurin hadiye tabar Wiwi da miyagun kwayoyi da aka kama shi da ita a hanyar kotu.

Tunda fari jami’an tsaron, sun kama matasahin da zargin samun sa da kayan maye, inda yake boye da wasu basu sani ba, kafin kuma a kai shi kotu, ya ciro su yana yunkurin hadiye wa.

Wakilin mu na ‘yan Zazu, Ibrahim Abdullahi Soron Dinki yana da cikakken rahoton.

Continue Reading

Trending