Connect with us

Labarai

Tsohon shugaban kasa Obasanjo ya dauki fasinjoji kyauta a Adaidaita Sahu

Published

on

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya tuka babur mai kafa uku, inda ya debi fasinjoji kyauta.

Obasanjo, ya bi ta wasu hanyoyi a Abeokuta, babban birnin Ogun, don daukar fasinjoji, lamarin ya dauki hankulan mutane da dama wadanda su ka yi wa tsohon Shugaban kasa murna tare da daukar hotunan sa.

Obasanjo wanda ya rinka daukae mutane kyauta  a ranar Asabar, ya zarce ta Moshood Abiola, NNPC Mega Station, Kasuwar Kuto, da dai sauransu.

Aikin wani bangare ne na shirin Keke na OBJ @ 85 na Cibiyar Bunkasa Matasa na Laburaren Shugaban Kasa na Olusegun Obasanjo (OOPL).

A cikin jawabinsa, Obasanjo ya yi kira ga matasa cewa kar su bar masu tada zaune tsaye.

Tsohon shugaban ya ce, duk da kalubalen da ake fuskanta, ya kamata su yi kokarin amfani da damar da ake da su domin yin tasiri ga al’umma.

“Dole ne matasa ku dunkule ku byar da gudummawa, domin ganin abubuwa su kasance kamar yadda ya kamata.

“Idan kun bar abubuwa ga masu yi muku almundahana sun cigaba da shugabanci, komai ba zai tafi daidai ba, domin ku ne shugabannin gobe, ba za ku taba samun haka gobe ba.

“Allah ya baka ikon zama abin da ke so ka zama. Idan kuka yanke shawara, Allah zai taimake ku ya samar da mutanen da za su taimake ku,”  A cewra Obasanjo.

Baba Suda

NNPP:- Kwankwaso ya sulhunta rikicin jamiyyar

Published

on

Rahotanni daga Abuja sun tabbatar da jagoran kwankwasiyya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi wani zama da Dan majalisar tarayya Mai wakiltar kananan hukumomin Rimin Gado, Tofa da Dawakin Tofa, Wato Honorable Abdulkadir Jobe, da kuma Daraktan yada labaran Gwamnan Kano Honorable Sunusi Bature Dawakin Tofa.

 

Ganawar wadda ta gudana a yammacin wannan Alhamis ta kawo karshen Jan Zaren dake faruwa tsakanin Dan majalisar da kuma Sunusi Bature.

 

A baya bayan nan dai an kai ruwa rana tsakanin su, Inda kowa ne bangare ke mayar da martani.

Abdulkadir Jobe da kuma Sunusi Bature dukkanin su mabiya jamiyyar NNPP ne tsagin kwankwasiyya.

Continue Reading

Labarai

Real Madrid ta kaddamar da Alexander

Published

on

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta ƙaddamar da ɗan wasa Trent Alexander Arnold a yau a matsayin ɗan wasan ta

Inda shugaban ƙungiyar Flerontino Perez yace yau suna matuƙar Farin ciki kasancewar sun mallaki babban ɗan wasan baya a duniya.

 

Shima ɗan Wasa Arnold ya bayyana cewa yana cikin farin ciki kuma mafarkin sa ya cika na zama ɗan Wasan Madrid a yau.

Continue Reading

Daurin Boye

Zan shiga kawancen ‘yan jamiyyar hamayya – tsohon Minista

Published

on

Tsohon ministan sufurin Najeriya, Rotimi Amaechi ya ce a shirye yake don shiga ƙawancen ƴan jamiyyar hamayya domin ƙalubalantar Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027

A wata hira da BBC, tsohon gwamnan na jihar Rivers ya ce suna ƙoƙarin samar da haɗakar siyasar da za ta samar da sauyi a ƙasar.

Amaechi wanda ɗan jam’iyyar APC ne  ya nuna damuwa kan abin da ya ƙira halin ƙuncin rayuwa da ƙasar ke ciki.

Amaechi ya ce bai cire tsammanin yin takarar shugaban ƙasa ba, illa lokaci ne kawai zai tantance.

Continue Reading

Trending