Connect with us

Siyasa

Kotu ta sake rushe zaben fidda gwani na gwamnan APC a Taraba

Published

on

Kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, ta soke zaɓen fitar da gwanin gwamna na jam’iyyar APC na jihar Taraba.

Alƙalin kotun mai shari’a Obiora Egwatu, ya ce, la’akari da hujjoji da shaidu da aka gabatar a gaban kotu, sun nuna cewa zaɓen fitar da gwanin da ka gudanar ranar 26 ga watan Mayun wannan shekara, wanda ya ayyana Sanata Emmanuel Bwacha a matsayin ɗan takarar ba halastacce ba ne.

A watan da ya gabata ne dai wata kotun tarayya a birnin Jalingo ta soke zaɓen fitar da gwanin da jam’iyyar ta yi wa mista Bwacha, sakamakon ƙarar da ɗaya daga cikin ‘yan takarar ya shigar a gaban kotun yana ƙalubalantar sahihancin zaɓen.

Duka kotunan biyu a hukunce-hukuncen da suka yi, sun bayar da umarnin ga uwar jam’iyyar da ta sake shirya wani sabon zaɓen fitar da gwani a jihar.

Siyasa

Rurum ya sanar da ficewa daga jam’iyyar NNPP zuwa APC a zauren Majalisar Wakilai

Published

on

Shugaban majalisar Wakilai ta Ƙasa Tajudden Abbas, ya karanta takardar ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Rano, Kibiya da Bunkure, RT. Honarable Kabiru Alhassan Rurum, ta ficewarsa daga Jam’iyyar NNPP zuwa Jam’iyyar APC, a hukumance.

Tajuddeen Abbas, ya karanta takardar sauyin sheƙar da Rurum din yayi a harabar Majalisar, a zamanta na yau Alhamis.

Wannan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da mai bai wa Rurum, shawara na musamman akan shafukan sada zumunta Fatihu Yusuf Bichi, ya fitar a ranar Alhamis 15-05-2025.

Tun dai a baya an jiyo yadda Honarable Kabiru Alhassan Rurum, ya sanar da ficewar sa daga jam’iyyar NNPP zuwa APC, wanda a yanzu na tabbatar da ficewar tasa a hukumance a zauren Majalisar Wakilai ta ƙasa.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau shugaban kasa zai dawo daga Faransa

Published

on

Bayan ziyarar aiki ta kusan mako biyu Zuwa kasar Faransa a yau litinin ake saka ran shugaban kasa zai dawo gida Nigeria.

Cikin sanarwar da hadimin shugaban kasar kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga ya fitar ya ce kowa ne lokaci daga yanzu shugaban kasa Asuwaju Bola Tinubu zai sauka a Nigeria domin cigaban da harkokin mulkin kasar.

Continue Reading

Hangen Dala

Kofar APC a bude take ga masu shiga – Abdullahi Abbas

Published

on

Jamiyyar APC a Jihar Kano tace Kofar ta a bude take ga dukkanin masu son shigowa jamiyyar.

 

Shugaban jamiyyar na Kano Hon Abdullahi Abbas ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai.

 

Abbas yace labarin dake yawo cewa akwai wadanda ke Shirin shigowa jamiyyar, su sani Kofar APCn a bude take tare da maraba ga dukkanin wadanda zasu shigo.

 

Koda dai Abdullahi Abbas yace shigowa APC ba zai hana tuhuma kan zargin cin hanci da rashawa ba, koma kaucewa hukumar EFCC da ICPC.

 

A baya bayan nan ne dai aka rinka yada cewa mabiya jamiyyar NNPP kwankwasiyya na Shirin shiga jamiyyar APC tare da madugun ta Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Continue Reading

Trending