Connect with us

Manyan Labarai

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar kafa masarautu uku masu daraja ta biyu a jihar

Published

on

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan ƙudirin dokar da ta kafa masarautu uku masu daraja ta biyu a jihar Kano.

Dokar da ta kafa masarautun uku masu daraja ta biyu, ya biyo bayan tsallake karatu na biyu da na uku yau a zauren majalisar dokoki ta jihar Kano, inda dokar ta ƙunshi masarautun Ƙaraye, wadda za ta jagoranci Rogo, sai Gaya da zata jagoran ci Albasu, da Ajingi, yayin da masarautar Rano za ta jagoranci Kibiya, da Bunkure.

Da yake jawabi yayin sanya hannun gwamna Abba Kabir Yusuf, ya ce nan ba da jimawa ba za’a bayyana sunayen sarakunan da za’a tura masarautun domin jagorantar yankunan.

Wakilinmu na fadar gwamnatin Kano Umar Abdullahi Sheka ya rawaito cewa, kakakin majalisar dokokin jihar Kano Honarable Isma’il Jibril Fargore, da tawagar sa ne suka jagoranci kai takardar ga gwamnan domin sanya hannu akan dokar.

Manyan Labarai

Babu ɗaga Ƙafa tsakanin mu da Ƴan Daba da masu ƙwacen Waya a Kano – Anty Snaching Phone

Published

on

Rundunar tsaron nan da ke yaƙi da faɗan Daba da ƙwacen Wayoyin jama’a da kuma daƙile Shaye-shayen kayan maye ta Anty Snaching Phone, ta gargaɗi matasan da suke addabar al’umma da faɗan Daba a cikin birnin jihar Kano, da su ƙauracewa hakan domin ba za su saurarawa dukkanin wanda ya faɗa komar su ba.

Kwamandan rundunar tsaron a jihar Kano Inuwa Salisu Sharaɗa, shi ne ya bayyana hakan a zantawar sa da gidan rediyon Dala FM, ya ce duk wanda suka kama da laifi musamman ma na faɗan Daba, ko ƙwacen waya ko kuma sha da dillancin kayan maye, za a ɗauki tsattsauran mataki akan sa.

 

“Babu ɗaga ƙafa tsakanin mu da masu ƙwacen Wayoyin jama’a, da Faɗan Daba, da kuma masu Sha da dallancin kayan Maye a jihar Kano, kuma duk wanda mu ka kama sai mun miƙa shi gurin da ya dace don ɗaukar Mataki, “in ji Inuwa Sharaɗa”.

 

Ya kuma buƙaci iyaye da su ƙara sanya idanu wajen kula akan shige da ficen ƴaƴan su, ta yadda za su zama ababen koyi a tsakanin al’umma.

Continue Reading

Manyan Labarai

Za’a hukunta duk ma’aikacin Shari’ar da aka samu da laifi – Babbar Jojin Kano

Published

on

Babbar jojin Kano mai Shari’a Dije Abdu Aboki, ta jaddada cewar kwamitin ladabtarwa na hukumar Shari’a a jihar, zai hukunta duk wani ma’aikaci a tsagin Shari’a matuƙar aka same shi da laifin cin-hanci da rashawa.

Mai Shari’a Dije Aboki ta bayyana hakan ne a yayin taron ƙarawa juna sani wanda hukumar shari’ar ta gudanar ranar Talata, a ɗakin taro na Murtala Muhammad Library da ke Kano.

Taron an shirya shi ne don tunasar da sabbin ma’aikatan Shari’a, akan nauyin da ya hau kan su don mayar da hankali sosai akan batun gujewa cin-hanci da rashawa.

Babbar mai Shari’ar Dije Abdu Aboki, ta bayyana cewar akwai takaddu masu ɗauke da lambobin wayarta da aka liƙe a bangon kotuna, kuma duk wanda aka yi wa ba dai-dai ba zai iya sanar da ita ta kan lambobin kuma za a dauki mataki akan duk ma’aikacin da aka samu da laifi.

Wakilin tashar Dala FM Kano, Yusuf Nadabo Isma’il ya ruwaito cewa, a yayin taron taron ma’aikatan Shari’a da al’umma da dama ne suka samu damar halarta.

Continue Reading

Hangen Dala

Rashin wuta: Muna cikin mawuyacin hali – al’ummar Kano, Katsina da Jigawa

Published

on

Al’ummar jihohin Kano, katsina da Jigawa na fuskantar yanayi mara dadi, Sakamakon karancin samun wutar lantarki daga hukumar KEDCO.

Al’ummar jihohin sun ce iya sa’o’i uku kacal suke samun wutar, wanda hakan ke haifar musu da nakasu a harkokin kasuwancin su.

Wani bincike da jaridar Daily Trust tayi ta ambato yadda masu kananan masana’antu irin su Walda, Cajin Waya, Kankara da masu sana’ar dinki da dai sauran kananan sana’o’i dake amfani da wutar lantarki sun shiga mawuyacin hali.

Kazalika rashin wutar ya shafi hatta bangaren ruwan sha, dama masu sana’ar sayar da Ruwa a irin yankunan Hotoro da sauran irin wuraren dake sayen ruwa, Inda yanzu haka ruwan yayi tashin gwauron zabi a kowace jarka.

Koda dai ana ta bangaren hukumar rarraba hasken wutar lantarkin me kula da shiyyar Kano, Katsina da Jigawa KEDCO sun nemi afuwar al’umma.

Idan za’a tuna dai a makon jiya ne Ministan Wutar lantarki yace ‘yan Nigeria Miliyan 150 na samun wadatacciyar wutar lantarki.

Sai dai kuma a jihohi irin su Kano, Katsina da Jigawa na bayyana damuwa kan karancin Wutar, Inda suka ce bata wuce ta sa’o’i uku suke samu a kowa ce rana.

Continue Reading

Trending