Manyan Labarai
Abin takaici ne yadda wasu jihohi har yanzu su ka gaza biyan ma’aikata sabon albashi – PRP

Jam’iyyar hamayya ta PRP a Najeriya, ta yi Allah wa-dai da yadda har kawo yanzu wasu jihohi a ƙasar suka gaza fara biyan ma’aikatan jahohin su mafi ƙarancin albashi, duk kuwa da cire tallafin man fetur da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi, ya jefa rayuwar al’umma cikin ƙuncin rayuwa.
Hakan na ƙunshe ne ta cikin saƙon sabuwar shekara mai ɗauke da sa hannun mataimakin shugaban Jam’iyyar PRP na Arewa maso Yammacin ƙasa Abba Sule Namatazu, ya fitar ga manema labarai a ƙarshen makon nan.
“Jam’iyyar mu tana sane da shirin gwamnatin Tarayya na mayar da wasu makarantu Gwamnati masu zaman kansu da hakan ka iya tilastawa matasa da dama barin Makaranta, inda wasu ka iya fadawa cikin halin aikata laifuka, baya ga yadda rashin tsaro ke kara ta’azzara zuwa sassan Najeriya, “in ji Namatazu”.
Har ila yau, jam”iyyar hamayya ta PRP, ta nuna takaicinta kan yadda har yanzu Najeriya ba ta samu wani ci gaban azo-a-gani ba cikin shekara 64 da samun ‘Yancin kai, da kuma shekara 25 na mulkin Demukuraɗiyya ba tare da katsewa ba.
Namatazu, ya kuma ce bisa la’akari da shekarun da aka shafe da samun ƴancin kai, kamata ya yi ace ƙasar nan ta fita daga cikin ƙasashen da ke fama da talauci da rashin tsaro da cin hanci da rashawa, Sai dai hakan bata sami ba saboda rashin Ingantaccen shugabanci a cikin shekaru 25 daga 1999 zuwa yanzu.
Abba Namatazu ya kuma yi kira ga Gwamnatoci a kowane mataki da su ƙara ƙaimi wajen inganta fannnin aikin Gona, da lafiya, da Ilimi, da kuma Tsaro da sauraran fannonin ci gaban Al’umma.
Jam’iyyar ta PRP ta kuma bukaci ‘Yan Najeriya da su tabbatar da Kyakkyawan Shugabanci da kuma bibiyar shugabannin su.

Baba Suda
Gwamnatin Kano ta musanta labarin da ke cewa za ta saka kafar Wando daya da Sojojin Baka

Gwamnatin jihar Kano ta musanta labarin da ke yawo na cewa za ta saka kafar wando daya da Sojojin Baka.
Kwamishinan yada labaran jihar Kwamred Ibrahim Waiya shi ne ya bayyana hakan lokacin wani taron karawa juna sani da hukumar kula da kafafen yada labarai NBC ta shirya a yau Alhamis.
Yace gwamnatin Kano za ta hada kai da Yan siyasa masu magana a Rediyo da aka fi Sani da Sojojin Baka, domin tsaftace harkokin siyasar Kano.
Haka kuma kwamishinan ya musanta labarin da ke cewa Gwamnatin Kano za ta saka kafar wando daya da Sojojin Baka.
Kwamishina Waiya ya kuma ce za su hada kai da kafafen yada labarai domin Kara kawo tsafta a harkokin siyasar Kano.

Manyan Labarai
Da Ɗumi-Ɗumi! Tinubu ya dakatar da gwamnan jihar Rivers da mataimakin sa da ƴan majalisar jihar na watanni 6.

Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya dakatar da gwamnan jihar Rivers Siminalayi Fubara, da mataimakiyar sa Mrs. Ngozi Odu, har na tsawon watanni 6.
Shugaba Tinubu ya bayyana daukar matakin ne a cikin wani taƙaitaccen jawabin sa da ya gabatar a cikin daren Talatar nan, ya ce ya yi amfani da damar da kundin tsarin mulki ya ba shi wajen sanya wannan doka wacce ta kwace mulkin jihar daga hannun gwamnan jihar Siminalayi Fubara da mataimakin sa har sai lamura sun dawo dai-dai a jihar.
Kazalika, shugaba Tinubu ya kuma bayyana dakatar da dukkanin ƴan majalisar dokokin jihar suma na tsawon watanni shidan, tare da sanya dokar ta ɓaci a jihar.
Wannan dai na zuwa ne biyo bayan rikicin siyasar da ya daɗe da kunno kai a tsakanin gwamna Fubara da ministan birnin tarayya Abuja Nyesome Wike, al’amarin da ya janyo takun saƙa tsakanin sa da ƴan majalisar dokokin jihar.

Manyan Labarai
Isra’ila ta kashe sama da mutane 200 bayan karya yarjejeniyar tsagaita Wuta a Gaza

Isra’ila ta keta yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, tare da ƙaddamar da sabbin hare-hare kan Falasdinawa.
Jaridar TRT Hausa ta ruwaito cewa, aƙalla Isra’ila ta kashe fiye da mutum 200 tare da jikkata ɗaruruwa a yayin da ake ci gaba da kai gawawwaki asibiti, kamar yadda majiyoyin wani asibiti a yankin Gaza suka bayyana.

-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai4 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi5 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su