Connect with us

Manyan Labarai

Barayin babura sun uzzurawa wata unguwa a Kano

Published

on

Wasu barayi masu yin sata a cikin dare sun uzzurawa al’ummar unguwar Kadawa MulTara dake karamar hukumar Ungogo da sace-sace.

Daga cikin barayin, an yi zargin akwai wani mutum dake sanya hijabi ya na haurawa gidajen mutane cikin dare a yankin, kuma da an yi masa ihun barawo sai ya sake kama katangar ya haura ta inda ya shigo ya koma, har ta kai ya shiga gidaje da dama ba’a kama shi ba, kamar yadda wata daga cikin matan aure a yankin ta shedawa Wakiliyarmu Marakisiyya Umar Kamshi.

Bayan kurar wannan mutum mai sanya hijabi ta lafa, sai kuma wasu sababbi su ka sake bulla a yankin, wadanda su kuma ake zargin su na bin dare su kwanta a cikin almjirai a makarantarsu ta allo, inda wani alamajiri ya lura da su ya kwarmata musu ihu sai suka fitar da adda su ka datsa masa hannu.

Sai kuma rukunin wadanda ake zargin, su na lura da masu sababbin babura su kuma gane gidajensu, idan dare ya yi sai su haura su dauke musu baburin, bayan kuma sun fita sai su kulle mutum ta baya.

Wakiliyar tamu ta kuma zanta da wani mutum wanda su barayin su ka dauke masa sabon Babur, su ka kuma kulle shi ta baya, kuma dake barci yake yi bai san sun dauka ba saboda ya rufe kofa, ya ce, “Sai da Asuba ta yi kawai sai na ji iska ta na shigowa, muna bude kofar dakin, sun dauke Baburin, sun tafi ba su rufe ba, amma sai suka kulle ni ta can kofar gida.” A cewar mai Babur.

Wadannan barayi dai an yi zargin har shaguna suke ballewa, kamar dai yadda suka takaita wani shagon provision a unguwar.

Malam Muntari Aliyu Kadawa shi ne Dagacin garin na Kadawa Mul Tara ya ce, “Zamu dauki matakin zagaya alkur’ani akan al’amarin, Kuma akwai bukatar mahukunta su shigo a dauaki mataki na tsaro.” Inji Muntari Kadawa.

 

Manyan Labarai

Za’a ɗauki mataki akan duk wanda yake da hannu Gini ya ruftawa mutane a Kuntau – Ƙaramar hukumar Gwale.

Published

on

Yayin da wani ginin Bene mai hawa biyu ya danne aƙalla sama da Leburori goma a unguwar Kuntau kusa da KEDCO, a safiyar yau Juma’a, Shugaban riƙo na ƙaramar hukumar Gwale Abubakar Mu’azu Mojo, ya ce za’a ɗauki mataki akan dukkan wanda aka samu da laifi har al’amarin ya faru.

Abubakar Mu’azu Mojo, ya bayyana hakan ne yayin zantawar sa da manema labarai, yayin da ya ziyarci gurin da lamarin ya faru lokacin da ake ci gaba da aikin ceto mutanen.

Mojo, ya kuma ce babu makawa za’a ɗauki matakin doka akan duk wanda aka samu da hannu akan faruwar lamarin, kama daga ɗan kwangilar da aka bai wa aikin ginin, zuwa kuma mamallakin gidan.

Rahotanni sun bayyana cewa zuwa tsakar ranar yau aƙalla mutane bakwa aka ciro daga ƙasan ginin shida daga cikin su basa iya motsa jikin su, yayin da hukumomi suka ci gaba da gudanar da aikin ceto sauran mutanen da ginin ya danne.

Continue Reading

Manyan Labarai

Sulhu da ƴan Bindiga ba zai haifar da Ɗa mai ido ba – Human Rights 

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta ƙasa da ƙasa wato International Human Rights Commission, ta ce sulhu da ƴan bindiga ba zai haifar da Ɗa mai ido ba a ƙasar nan.

Babban daraktan ƙungiyar Kyaftin Abdullahi Bakoji Adamu mai ritaya, shi ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da gidan rediyon Dala FM Kano.

Ya ce kasancewar ƴan bindigar basu da wata manufa bai kamata ayi sulhu da su ba, mai-makon hakan yafi dacewa a rinƙa ɗaukar tsauttsauran mataki akan su duba da yadda suke cutar da al’umma.

Ya kuma ce batun da mai bai wa shugaban ƙasa akan sha’anin tsaro Malam Nuhu Ribaɗo, ya yi a baya baya nan, kam cewar an fara samun fashimtar juna da wasu daga cikin ƴan Bindigar da suka addabi mutane a sassan ƙasar nan, a wani ɓangare ma kama da yin sulhu da su, ya faɗi hakan ne kawai amma hakan ba zai haifar da Ɗa mai ido ba.

Continue Reading

Manyan Labarai

Gwamnatin Kano ta kulle wata makaranta mai zaman kan ta a jihar

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta rufe wata makaranta mai suna Golden Crown International School a jihar, da ke yankin Sabon gari, bisa zargin an fake da sunan makarantar ana haɗa magani mara inganci mai-makon koyar da karatu a ciki.

Shugaban kwamitin yaki da miyagun ƙwayoyi da ƙwacen waya na jihar Kano General Gambo Mai Aduwa Mai ritaya, ne ya bayyana hakan, a lokacin da Kwamitin ya kai wani sumame da karfe uku da rabi na daren jiya Talata.

Rahotanni sun bayyana cewa makarantar tana kan titin Zungero da ke cikin ƙaramar hukumar Fagge a jihar Kano, wanda bayan samun bayanan sirri aka ɗauki matakin kulle ta.

Mai Aduwa, ya ƙara da cewar tsarin gurin ta waje ya nuna makaranta ce amma kuma sai ake sarrafa magani da ake zargin ingancin sa da bai kai yadda ya kamata ba, tare da ajiye Allurai da kayan haɗa magani cikin ajujuwan mai-makon ɗalibai.

“Za mu faɗaɗa bincike akan al’amarin dan sanin matakin da za mu ɗauka na gaba, “in ji shi”.

Suma masu gadin gurin da muka zanta da su sun bayana cewar, aikin gadi kawai suke yi amma basu da masaniyar abubuwan dake gudana a cikin makarantar, da ake zargin ana sarrafa magani mara ingani da ajiye shi a muhalin da ake zargin bai yi dai-dai da tsarin doka ba.

Wakilinmu Abba Isah Muhammad ya rawaito cewa shugaban kwamitin ya ce, zai ci gaba da bibiyar guraren dake yin abubuwan da za su kawo koma baya ga harkokin lafiya, da ci gaban jihar Kano, musmman wajen yaƙi da miyagun ƙwayoyi da ƙwacen waya.

Continue Reading

Trending