Connect with us

Labarai

Kwamitin Ganduje zai fara Zama domin sauraren koken mambobin jam’iyyar APC.

Published

on

Shugaban kwamitin sasancin rikicin cikin gidan jam’iyyar APC a Kano, Gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya ce kwamitin ya kammala duk wani shiri, domin dai fara sauraren koken mambobin jam’iyyar.

Hakan dai na kunshe ne cikin wata takarda mai dauke da sa hannun kwamishinan yada labarai, Malam Muhammad Garba ya fitar, inda ya ce kwamitin zai fara zama, domin sasanta mambobin jam’iyyar APC daga gobe Juma’a 11 ga wannan wata.

Ta cikin sanarwar, Ganduje ya tabbatar da cewa, za su yi duk mai yiyuwa, wajen ganin an sasanta rikicin jam’iyyar a nan Kano.

Jam’iyyar APC Kano dai na fama da rikicin cikin gida, tsakanin bangaren Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje da kuma tsagin Sanata Malam Ibrahim Shekarau, ( G7 ), wanda har ta kai uwar jam’iyya ta kasa ta rushe zabukan shugabannin APC tare da sanya Gwamna Ganduje da ya jagoranci wani kwamiti, domin dinke barakar jam’iyyar, lamarin da tsagin G7 suka ki aminta da shi.

Baba Suda

NNPP:- Kwankwaso ya sulhunta rikicin jamiyyar

Published

on

Rahotanni daga Abuja sun tabbatar da jagoran kwankwasiyya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi wani zama da Dan majalisar tarayya Mai wakiltar kananan hukumomin Rimin Gado, Tofa da Dawakin Tofa, Wato Honorable Abdulkadir Jobe, da kuma Daraktan yada labaran Gwamnan Kano Honorable Sunusi Bature Dawakin Tofa.

 

Ganawar wadda ta gudana a yammacin wannan Alhamis ta kawo karshen Jan Zaren dake faruwa tsakanin Dan majalisar da kuma Sunusi Bature.

 

A baya bayan nan dai an kai ruwa rana tsakanin su, Inda kowa ne bangare ke mayar da martani.

Abdulkadir Jobe da kuma Sunusi Bature dukkanin su mabiya jamiyyar NNPP ne tsagin kwankwasiyya.

Continue Reading

Labarai

Real Madrid ta kaddamar da Alexander

Published

on

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta ƙaddamar da ɗan wasa Trent Alexander Arnold a yau a matsayin ɗan wasan ta

Inda shugaban ƙungiyar Flerontino Perez yace yau suna matuƙar Farin ciki kasancewar sun mallaki babban ɗan wasan baya a duniya.

 

Shima ɗan Wasa Arnold ya bayyana cewa yana cikin farin ciki kuma mafarkin sa ya cika na zama ɗan Wasan Madrid a yau.

Continue Reading

Daurin Boye

Zan shiga kawancen ‘yan jamiyyar hamayya – tsohon Minista

Published

on

Tsohon ministan sufurin Najeriya, Rotimi Amaechi ya ce a shirye yake don shiga ƙawancen ƴan jamiyyar hamayya domin ƙalubalantar Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027

A wata hira da BBC, tsohon gwamnan na jihar Rivers ya ce suna ƙoƙarin samar da haɗakar siyasar da za ta samar da sauyi a ƙasar.

Amaechi wanda ɗan jam’iyyar APC ne  ya nuna damuwa kan abin da ya ƙira halin ƙuncin rayuwa da ƙasar ke ciki.

Amaechi ya ce bai cire tsammanin yin takarar shugaban ƙasa ba, illa lokaci ne kawai zai tantance.

Continue Reading

Trending