Manyan Labarai
Zauren hadin kan malaman jihar kano ya ja hankalin yan jihar dasu gudanar da zaben 2023 lafiya

Zauren haɗin kan malaman jihar Kano yayi kira ga mazauna jihar nan da su gudanar da zaɓen 2023 cikin kwanciyar hankali tare da kaucewa tayar da tarzoma.
Sakataren zauren haɗin kan malaman na Kano Dakta Sa’idu Ahmad Dukawa ne ya bayyana hakan, ta cikin wani saƙon murya da ya aikowa Dala FM, da yammacin Alhamis ɗin nan.
Zauren haɗin kan malaman ya kuma yi kira ga al’umma da su zaɓi wanda ya kwanta musu cikin kwanciyar hankali, tare kuma da gujewa duk wani nau’i na fitina domin takan shafi mutanen da ba ruwansu.
Ya kuma ce yana daga cikin hikima yin zaɓe wajen samar da shugabanci ko kuma sauyashi, inda ya kuma yi kira ga limamai da su sanya ƙasa cikin addu’o i yayin gabatar da huɗubar Juma’ar da za su gabatar a gobe juma’a da sauran lokutan Sallah, domin samun shugabanni na gari.
An cire Naja’atu Muhammad daga harkokin kula da ‘yan sanda a lokacin zabe
Wannan dai na zuwa ne kwanaki biyu gabanin fara fita babban zaɓen 2023 a ranar Asabar.

Labarai
Mu yawaita karanta Alƙur’ani da aikin alkhairi a watan Ramadan – Malam Ibrahim Bunkure

Limamin masallaacin Juma’a na Salafussalih dake unguwar Ɗorayi ƙarama Malam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’ummar musulmi da su ƙara himma wajen karanta Al-ƙur’ani mai girma, tare da aikata ayyukan alkhairi domin rabauta da rahamar Allah S.W.T a nan duniya dama gobe ƙiyama.
Mallam Ibrahim Bunkure ya bayyana hakan ne lokacin da yake tsokaci kan huɗubar Juma’ar da ya gabatar yau a masallacin.
Ya ce, kamata yayi musulmai su ƙara yin koyi da kyawawan ɗabi’un Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi Wasallama, domin zama ababen koyi a rayuwa.
Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewar Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya kuma shawarci al’umma da su ƙara kasancewa masu yafiya musamman a lokacin da aka yi mutu abinda bai musu daɗi ba, bisa mahimmancin da hakan yake da shi.

Manyan Labarai
Gawuna ya taya Abba Gida Gida murna

Dan takarar Gwamnan Kano na jam’iyyar APC a zaben 2023 Dakta Nasiru Yusuf Gawuna ya bayyana karbar kaddara tun bayan da ya Fadi zaben 18 ga watan Maris.
Cikin Wani Sakon murya, Dakta Nasiru Gawuna ya godewa magoya baya, tare da yin fatan alkhairi ga sabuwar gwamnati.
” Wannan sabuwar gwamnati Allah ya Bata ikon yiwa al’umma adalchi, mu Kuma Allah ya bamu ikon yin biyayya.”
Manyan Labarai
Abba Gida Gida ya karbi shaidar lashe zabe

Sabon zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabiru Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida gida ya karbi shaidar lashe zaben Gwamnan Kano.
Ya karbi wannan shaida ce yayin wani taro da hukumar INEC ta shirya domin bashi shaidar satifiket, bayan nasarar da ya samu a zaben ranar 18 ga watan Maris 2023.
Taron dai Wanda ya samu halartar da dama daga cikin manyan jihar Kano dama shiyyar arewa maso yamma, ya gudana ne a dakin taro na ofishin hukumar zabe INEC na jihar Kano.
-
Nishadi3 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Manyan Labarai3 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai3 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Nishadi3 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai2 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Lafiya10 months ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Nishadi3 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
-
Manyan Labarai3 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano