Connect with us

Labarai

Yanzu-yanzu: Gobara ta tashi a kasuwar Kantin Kwari

Published

on

Wata gobara ta tashi yanzu haka a gidan alaramma dake kasuwar Kantin Kwari a nan Kano.

Gobarar dai ta tashi ne a daren yau Jumu’a jim kadan bayan sallar isha’i, sanadiyar wutar lantarki.

Wakilin mu Abba Isah Muhammad ya rawaito mana cewa shugaban kasuwar Alhaji Abba Muhammad Bello ya tabbatar da faruwar al’amarin inda yace gobarar ta cinye shago guda daya.

Tuni dai jami’an hukumar kashe gobara ta jihar Kano suka samu nasarar kashe wutar.

Labarai

Mai tallan magani ya shiga hannun hukumar Hisba

Published

on

Wasu mutane ne sun kai rahoton wani mai tallan maganin gargajiya a lasifika wato amsakuwa zuwa wurin hukumar Hisba, kan yadda yake fadar zantuka marasa ma’ana, ba tare da yana sakawa bakin nasa linzami ba.

Sai dai idan ya fada a lokacin da matar aure taje wucewa, suka kuma hada ido da matashi ko yaro, ko kuma wani babban mutumin, sai su kau da kai ko a rintse ido.

Mataimakin babban Kwamandan hukumar ta Hisba kan ayyuka na musamman Muhammad Albakari Mika’il, hukumar ta kai sumame, ta kuma samu nasarar kamo shi, ya kuma ce, “Koda mu ka buncika sai ga shi har da wani itace da ya sassaka sura, kuma mun ja hankalinsa akan tallan da ya ke yi dama irin abubuwan da ya ke fada iyayen wasu dama matan aure masu wucewa su na ji, don haka ko zai ya yin irin tallan, a gaban nasa mahaifan?”  Inji Albakari

Hukumar ta sake buncikawa, ta gano cewar, ashe ma bashi da aure, bai kuma taba yi ba, don haka aka ce to ya akai ya san rayuwar ma’auratan har ma yake tallan magani a kanta, wanda ya ce, “A wurin iyayen gidansa ya koyi sana’ar tallan maganin ya san irin sirrukan dake cikin zamantakewar auren.”  A cewar Tallan magani.

 

 

Continue Reading

Labarai

Masu kungiyoyin sa kai su guji shiga siyasa- Khalil Gabasawa

Published

on

Shu gaban majalisar matasa dake jihar Kano, Khalil Yusif Gabasawa, ya yi kira ga ‘yan kungiyoyin sa kai, su kara kaimi wajen tallafawa al’umma ba tare da gajiyawa ba, domin rayuwarsu ta zama abar koyi.

Khalil Yusif, ya furta hakan ne a yayin da Gidauniyar Saye Vocational Center, ta gudanar da taron yaye matasa kimamin Saba’in Maza da Mata da Gidauniyar ta koyawa sana’o’in dogaro da kai, wanda ya gudana a unguwar Saye a yankin karamar hukumar Nasarawa dake jihar Kano.

Ya kuma kara da cewa, “Tallafawa al’ummar da ‘yan kungiyoyin zai sanya al’ummar ta kai gagaci, kuma ‘yan kungiyoyin su guji sanya kansu cikin jami’iyyun siyasa.” Inji Gabasawa.

Da ya ke nasa jawabin, shugaban Gidauniyar, Yusha’u Abdu Ahmad Saye, jan hankalin gwamnati ya yi wajen tallafawa Kungiyoyin sa kai domin gudanar da ayyukan su ba tare da fuskantar matsala ba.
Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u, ya rawaito cewa, Matasan an koyar dasu sana’o’in dogaro da kai, wadanda su ka hadar da sana’ar dinki, da sana’a rhada jakunkuna, da kuma kayan kwalliya.

Continue Reading

Labarai

Marubuta su bunkasa harshen Hausa -Ibrahim Khalil

Published

on

Shugaban majalisar malamai ta Jihar Kano, Malam Ibrahim Kalil, ya bukaci Kungiyoyin marubuta da manazarta wakokin Hausa, su mayarda hankali wajen bunkasa al’adun Hausa.

Malam Ibrahim Kalil, ya bayyana hakan ne a yayin ziyarar da Kungiyar marubuta da manazarta suka kai masa a ofishin majalisar malaman dake kan Titin Court Road a jihar Kano.

Ya kuma ce,“Majalisar malamai ta Jihar Kano na mara ba da kowanne bangaren al’umma, domin ganin an inganta al’adun Bahaushe da suke tafiya tare da addini.” A cewar Ibrahim Khalil.

A nasa jawabin, shugaban kungiyar marubuta da manazarta wakokin Hausa na jihar Kano, Ibrahim Hamisu, ya ce, “Makasudin ziyarar shi ne kyautata alaka tsakanin kungiyar da majalisar Malan ta Jihar Kano.”  Inji Ibrahim.

Wakilin mu Abba Isah Muhammad, ya rawaito cewa, kungiyar ta kuma ja hankalin marubuta wajen yin rubutu kan hanyoyin da za su kawo cigaban ingantuwar al’adar Hausawa da tarbiya tsakanin yara masutasowa.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish