Connect with us

Labarai

ICPC ta bukaci a mikawa kananan hukumomi ayyaukan mazabun da aka kammala

Published

on

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa da dangoginsu ICPC ta yi kira da a mikawa kananan hukumomi duk wasu ayyukan mazabun da aka kammala don baiwa al’umma damar amfanarsu yadda ya dace.

Shugaban hukumar Farfesa Bolaji Owasanoye ne ya bayyana hakan a Abuja yana mai cewa da dukiyar al’umma aka yi ayyukan, a don haka wajibi ne a mika musu kayansu don gajiyarsu yadda ya kamata.

Wannan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babbar jami’ar yada labran hukumar Rasheedat Okoduwa.

Sanarwar ta kara da cewa hukumar ta gano cewa wasu ayyukan da aka kammala ba su da ingancin da ya kamata, a don haka ne ta ce ba za ta saurara ba a kokarin da ta ce na bibiyar ayyukan mazabun da ‘yan majalisa ke gudanarwa don tabbatar da kammala su.

Farfesa Owasanoye ya tabbatar da cewa ya zuwa yanzu an kammala kashi 60 cikin dari na ayyukan mazabun da aka bayar a fadin kasar nan, kuma wajibi ne jama’a su rinka bibiyar yadda ake gudanar da ayyukan.

A na sa bangaren Darakta janar na hukumar wayar da kan jama’a ta kasa Dr. Garba Abari, ya ce matukar mutane suka bibiyi yadda ake gudanar da ayyukan to babu shakka babu wani dan kwangila da zai yi algus wajen aikinsa.

 

Continue Reading
Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Labarai

Kotu zata yanke hukunci kan tsofafin shugabannin karamar hukumar Warawa

Published

on

Kotu ta sanya ranar yanke hukunci kan tsofafin shugabannin karamar hukumar Warawa da ake zargi da aikata ba dai-dai ba.

Kotun majistret mai lamba 15 karkashin mai Sharia Muntari Garba Dandago ta sanya ranar 16 ga watan gobe dan zartas da hukunci a kunshin tuhumar da ‘yansanda suke yiwa tsofafin shugabaninn karamar hukumar Warawa.

Wadand ake tuhuma sun hada  Ibrahim Abdullahi da Shehu Shazali wadanda ake zargi da lefin hada baki da yunkurin tayar da hankali da kuma lefin buga takardun jabu dangane da gonakin manoma na yankin katarkawa.

Wajibi ne bin umarnin kotu idan har ta bayar da umarni- Lauya

Kotu ta dakatar da Ganduje daga sabuwar dokar majalisar masarautar Kano

Buhari yayi nasara a kotun Koli.

wakilin mu  Yusuf Nadabo ya rawaito cewar, sai dai a yayin da ake karanta kunshin tuhumar dukkanin su, sun musanta zargin.

 

Continue Reading

Labarai

Ana zargin matashi da aikata kisan kai

Published

on

Kotun majistret mai lamba 58 karkashin mai shari’a Zubairu Inuwa ta aike da wani matashi gidan gyaran hali.

‘yan sanda sun gurfanar da matashin mai suna Felix Abah wanda ake tuhumar sa da aikata kisan kai.

Kunshin tuhumar ya bayyana cewar tun a ranar 6/4/2017 Felix ya gayyaci wani mai koyar da tukin mota mai suna Sani Abbas dan ya koya masa mota, amma daga karshe sai ya hallakashi ya gudu da motar ya sayar da ita miliyan daya da dubu dari bakwai.

A karshe kuma ya mika kansa caji ofis yayi ikirari a gaban ‘yansanda cewar shine ya hallaka Sani.

Kotun ta sanya ranar 10/1/2020 dan jiran shawararar lauyoyin gwamnati.

Wakilinmu yusuf Nadabo Ismail ya zanta da mahaifiyar Sani wadda tace tun lokacin da aka kashe sani bata da kwanciyar hankali.

Shima Felix ya bayyana cewar ya mika kansa caji ofis ne sakamakon rashin nutsuwar da ya shiga tun lokacin da yayi kisan.

Continue Reading

Labarai

DW ta baiwa Freedom Radio sabbin Babura don inganta ayyukansu

Published

on

Shugaban sashin hausa na gidan radion DW Thomas Mosh, ya ce kyautata alaka tsakanin kafafen yada labarai na duniya zai kawo cigaba ta fannin aikin jarida.

Thomas Mosh, ya bayana hakan ne lokacin da yake mika makullin babura masu kafa biyu, guda hudu ga janar manajan gungun rukunin tashoshin Freedom Radio da yammacin Yau alhamis, a shelkwatar Freedom Radio dake unguwar Sharada a birnin Kano.

Moshe, ya kara da cewar DW ta bayar da baburan ne ga Freedom Radiyo Kaduna dan kara zaburar da ma’aikatanta musamman sashin wasanni.

Da yake nasa jawabin bayan karbar baburan janar manaja, na Freedom Radio Malam Adamu Isma’ila Garki, cewa yayi hakan zai kara inganta aikin tashar kasancewar dama akwai yarjejeniyar aiki tare.

Wakilinmu Abba Isah Muhammad, ya ruwaito cewa hukumar gudanarwa ta Freedom Radio da Dala Fm Kano sun mika Kyauta ga shugaban sashin hausan na tashar DW, haka kuma shugaban tashar Freedom Radio Kano Malam Ado Saidu Warawa, da na Dala Fm Kano Ahmad Garzali Yakubu, da sauran shugabanni na daga cikin wadanda suka kasance a gurin taron.

 

Continue Reading

Trending

en_USEnglish
en_USEnglish