Connect with us

Manyan Labarai

Gudaji Kazaure ya soki kasafin kudin bana.

Published

on

Cikin jawabai ko tsokaci da ya saba gudanar wa, wakilin kazaure da yan kwashin jihar Jigawa a majalisar kasa Honarabul Muhammad Gudaji ya bayyana takaicin sa game kasafin kudin bana, bayan da majalisar ta amince dashi.

Gudaji kazaure yace abin takaici ne yadda kunshin kasafin kudin bana ya mayar da hankali kan manyan ayyuka, wanda a cewar sa ba shine bukatar talakawan kasarnan ba.

A cewar Gudaji ba hanya ce bukatar yan najeriya wanda mafi yawansu talakawa ne ba, a basu aikin da zasu samu kudin shiga a duk karshen wata shine mafi soyuwa.

Wakilin yaja hankalin majalisar ta tuna abinda ya faru lokacin da ake rajistar daukar aiki a rundunar civil defence, inda sama da mutane miliyan uku suka yi rajista, a guraben da basu wuce dubu goma ba.

Gudaji kazaure yayi mamakin inda hankalin shugabanni akan lakabin da aka yiwa kasafin kudin, wato kasafin gyara kasa, wanda sunan sa ya sha ban ban da abinda ya kunsa.

Ya jaddadawa shugaban majalisar cewa daukar aiki a halin da ake ciki yafi ginin hanyoyin da ba zasu amfanawa rayuwar talaka komai ba.

Muna ganin gwamnatoci na ginin hanyoyi da gadoji, shi mutane zasu ci su kwana?”

Yace irin wannan ce ke haifar da aikata manyan laifuka, tunda mafi yawan wadanda ake kamawa sun kammala karatun jami’a babu aikin yi.

A ganin sa ba dai dai bane rage yawan matasa da za’a dauka aikin jami’an tsaro na civil defence daga dubu goma zuwa dubu biyar.

Manyan Labarai

Ba za mu amince da yadda ake yawan kai wa jami’an mu hari ba a Kano – KAROTA

Published

on

Hukumar kula da zirgar-zirgar ababen Hawa ta jihar Kano, KAROTA, ta ce ba za ta lamunta da yadda ake yawan kai wa jami’anta farmaki ba, na ba gaira babu dalili yayin da suke gudanar da ayyukan su.

Shugaban Hukumar KAROTA, a Kano, Injiniya Faisal Mahmud Kabir, ne ya yi wannan gargaɗin ta cikin sanarwar da kakakin hukumar Abubakar Ibrahim Sharada ya aikowa tashar Dala FM Kano, a ranar Laraba 09 ga watan Afrilun 2025.

“Hakan na zuwa ne biyo bayan wani mummunan hari da wasu mutane da ke cikin baburin Adai-daita sahu suka kai wa jami’an na mu yayin da suke tsaka da aikinsu a titin da ke dab da gidan Buhari kan hanyar zuwa Gidan Zoo, “in ji shi“.

Sanarwar ta ce, tunda farko an tsayar da wani mai baburin Adai-daita Sahu ne inda yaƙi tsayawa, sai kawai aka hango mai ɗan sahun ya naushi jami’in karotar.

Sai dai a ta bakin Shugaban kungiyar ‘Yan Adai-daita Sahu a jihar Kano, ya ce waɗannan mutane ba halattattun ‘Yan Adai-daita Sahu ba ne, sun dai fake da sana’ar su dan aikata ta’addanci.

Daga bisani dai jami’n hulɗa da jama’a na Hukumar Koratar, Abubakar Ibrahim Sharada, ya ce hukumar za ta ɗauki tsattsauran mataki akan lamarin, don kare afkuwar irin hakan a gaba.

Hukumar ta ce duk wanda ya ga faruwar wani abu da ya shafe ta, ko kuma ƙorafe-ƙorafe, zai iya kiran waɗannan lambobin domin sanar da ita, da suka haɗar da 09015709449 ko 08059689422 ko kuma 08067311520.

Continue Reading

Manyan Labarai

Ɗan Bijilante ya rasa ransa bisa arangamar su da wasu ƴan Daba a Kano

Published

on

Ƙungiyar sintirin Bijilante ta ƙasa reshen jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin kwamandan ta Ubale Barau Muhammad Badawa, ta tabbatar da rasuwar guda daga cikin jami’in ta mai suna Suraj Rabi’u mazaunin Jaba da ke ƙaramar hukumar Fagge a jihar, sakamakon arangama da ƴan Daba.

Mai magana da yawun ƙungiyar Bijilante na jihar Kano, kuma Kwamandan ta na ƙaramar hukumar Fagge, Usman Muhammad Ɗan Daji, shi ne ya bayyana hakan ta cikin wani saƙon murya da ya aikowa Dala FM Kano a ranar Lahadi.a

“Jami’in Bijilanten namu ya rasa ran nasa ne sakamakon arangama da suka yi da wasu Ƴan Daba yayin gudanar aikinsu a ranar Idin ƙaramar Sallah, inda ƴan dabar suka soke shi da Ɗanbida a Ƙirji da bayansa, wanda ya yi sanadiyar rasuwarsa, “in ji Usman”.

Ya kuma ce, an kama ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi mai suna Usman Sharif mazaunin ƙaramar hukumar Dala, kuma tuni aka miƙa shi hannun jami’an tsaro.

Usman Ɗan daji, ya kuma yi addu’ar Allah ya jiƙan jami’in nasu ya gafarta masa.

Continue Reading

Manyan Labarai

An ga watan ƙaramar Sallah a Najeriya – Sarkin Musulmi

Published

on

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na uku ya tabbatar da ganin jinjirin watan Shawwal a Najeriya, inda za a yi karamar Sallah gobe Lahadi.

Sarkin Musulmin ya bayyana hakan ne a yayin jawabin da ya gabatar a cikin daren Asabar ɗin nan, ya ce sun samu rahotannin ganin watan ne daga sassa daban-daban na ƙasar nan.

Alhaji Sa’ad Abubakar ya ce daga cikin guraren da aiko musu da ganin jinjirin watan na Shawwal akwai Zazzau, da kuma daga Sarkin Dutse, da Arugungu, da kuma Shehun Borno, da dai sauran gurare daban-daban na Najeriya.

Ya kuma yi kira ga al’ummar Musulmi da su gabatar da bikin sallar cikin kwanciyar hankali, tare da taimaka wa mabuƙata.

Tashar Dala FM Kano ta ruwaito cewa, biyo bayan sanarwar fadar mai alfarma Sarkin Musulmi, ya kasance ranar Lahadi take 1 ga watan Shawwal na shekarar 1446, wato ranar ƙaramar Sallah.

Continue Reading

Trending