Connect with us

Manyan Labarai

Masarautar jihar kano ta koma kotu.

Published

on

Wasu lauyoyi anan karkashin jagorancin Barrister Abubakar Balarabe mahmud sun shigar da kudiri gaban babbar kotun jiha mai lamba 3.

kudirin nasu ya dogara da tanadi na 38/1, da kuma tanadi na 39 wanda ya kafa babbar kotun jiha ya kuma bata hurumin sauraron sauraron wannan roko.

Shariar mai kunshe da lamba k/197/2019
Wadda Yusuf Nabahani madakin kano, da Abdullahi sarki makaman kano, da Bello Abubakar sarkin Dawaki mai tuta da muktar Adnan sarkin Ban Kano suka shigar, suna karar gwamnan kano da shugaban majalisar dokokin kano da majalisar dokokin jihar da babban baturen Sharia da Tafida Abubuakr Ila da Ibrahim Abdulkadir Gaya da Dr Ibrahim Abubakar da Aminu Ado Bayero.

Rukon da masu kara sukayi Sun bukaci kotun da ta dakatar da wanda ake kara na 1 da na 2 da na 2 da na 4 ko dai su da kansu, ko kuma yan Korensu, su dakata daga yin wata doka ko ci gaba da ita ko tursasawa ko ci gaba da tursawa akan dokar tsaga masarauta.

Lauyoyin a madadin masu kara suna rokon a dakata har zuwa kammala shari’ar.

A sadara ta biyu cikin rokon Sun bukaci dakatar da wadanda ake kara na 1 zuwa na 4 ko su da kansu, ko yan korensu, ko hadiman su da su daina ayyana wadanda ake kara na 5 da 6 da na 7 da na 8 a matayin da dokar ta ayyanasu har zuwa karshen shari ar.

Sadara ta uku sun roki na 5 zuwa na 8 ko dai su da kansu ko yan korensu ko hadimansu da su daina bayyanasu a matasiyin sarakuna tunda dokar da ta kirkiresu ita ce kano state 2019 wadda wannan maganar dama tun tuni tana gaban wannan kotu mai girma a jira kuma jin ra ayin kotun.

Sadara ta 4 Sun roki kotun ta dakatar da gwamna daga daukar duk wani mataki ko canzawa sarkin Kano wata masarauta 8.

Sadara 6 lauyoyin Sun roki a dakatar da shugaban majalisar sarakuna ko shi da kansa ko yan korensa ko hadimansa daga shiga duk wata tattaunawa ta waccan da waccan doka ta tanada tun har zuwa karshen shariar.

Sai kuma sadarar da ta roki a dakatar da gwamna daka bikin nada sarakunan da waccan doka ta tanado tun da maganar tana gaban kotu.

Wakilin mu a kotu Yusuf Nadabo Ismail ya ruwaito cewa kotun ta sanya ranar 17 ga wannan watan domin fara sauraron wannan kudiri.

Idan dai zaa iya tunawa a makon daya gabata ne majalisar dokokin jihar kano ta amince da sabuqar dokar kafa masarautu 4 karkashin sarakunan yanka, bayan da kotu ta haramta irin wannan yunkuri a cikin watan 11 na shekarar dake bankwana.

Manyan Labarai

Ɗan Bijilante ya rasa ransa bisa arangamar su da wasu ƴan Daba a Kano

Published

on

Ƙungiyar sintirin Bijilante ta ƙasa reshen jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin kwamandan ta Ubale Barau Muhammad Badawa, ta tabbatar da rasuwar guda daga cikin jami’in ta mai suna Suraj Rabi’u mazaunin Jaba da ke ƙaramar hukumar Fagge a jihar, sakamakon arangama da ƴan Daba.

Mai magana da yawun ƙungiyar Bijilante na jihar Kano, kuma Kwamandan ta na ƙaramar hukumar Fagge, Usman Muhammad Ɗan Daji, shi ne ya bayyana hakan ta cikin wani saƙon murya da ya aikowa Dala FM Kano a ranar Lahadi.a

“Jami’in Bijilanten namu ya rasa ran nasa ne sakamakon arangama da suka yi da wasu Ƴan Daba yayin gudanar aikinsu a ranar Idin ƙaramar Sallah, inda ƴan dabar suka soke shi da Ɗanbida a Ƙirji da bayansa, wanda ya yi sanadiyar rasuwarsa, “in ji Usman”.

Ya kuma ce, an kama ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi mai suna Usman Sharif mazaunin ƙaramar hukumar Dala, kuma tuni aka miƙa shi hannun jami’an tsaro.

Usman Ɗan daji, ya kuma yi addu’ar Allah ya jiƙan jami’in nasu ya gafarta masa.

Continue Reading

Manyan Labarai

An ga watan ƙaramar Sallah a Najeriya – Sarkin Musulmi

Published

on

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na uku ya tabbatar da ganin jinjirin watan Shawwal a Najeriya, inda za a yi karamar Sallah gobe Lahadi.

Sarkin Musulmin ya bayyana hakan ne a yayin jawabin da ya gabatar a cikin daren Asabar ɗin nan, ya ce sun samu rahotannin ganin watan ne daga sassa daban-daban na ƙasar nan.

Alhaji Sa’ad Abubakar ya ce daga cikin guraren da aiko musu da ganin jinjirin watan na Shawwal akwai Zazzau, da kuma daga Sarkin Dutse, da Arugungu, da kuma Shehun Borno, da dai sauran gurare daban-daban na Najeriya.

Ya kuma yi kira ga al’ummar Musulmi da su gabatar da bikin sallar cikin kwanciyar hankali, tare da taimaka wa mabuƙata.

Tashar Dala FM Kano ta ruwaito cewa, biyo bayan sanarwar fadar mai alfarma Sarkin Musulmi, ya kasance ranar Lahadi take 1 ga watan Shawwal na shekarar 1446, wato ranar ƙaramar Sallah.

Continue Reading

Manyan Labarai

Shugaba Tinubu da Sifeton Ƴan Sanda ku bi wa mutanen mu da aka yi wa kisan gilla hakƙin su – Rt. Hon. Rurum

Published

on

Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Rabo, Kibiya da Bunkure, Kabiru Alhassan Rurum, ya bayyana kaɗuwar sa bisa kisan gillan da aka yi wa wasu Mafarauta su kusan 16, a garin Uromi da ke jihar Edo, a lokacin da suke hanyar su ta komawa Kano daga jihar Rivers.

Honarable Kabiru Rurum, ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da aka aikowa Dala FM Kano a ranar Asabar, ya ce daga cikin mutanen da aka ƙona akwai mutum 11 da suka fito daga mazaɓun yankin sa na Kibiya da Bunkure, inda wasu 6 suka samu muggan raunuka suna karɓar Magani yanzu haka a jihar Edo.

A cewar Ɗan Majalisar, “Wannan abu da matasan garin Uromi a jihar Edo, suka yi ya saɓa da dokar kasa, kuma mummunan laifi ne, a don haka za mu bi kadin hakƙin mutanen mu da aka kashe a kuma waɗanda aka jikkata, “in ji shi“.

Kabiru Rurum, ya ce a matsayinsa na wakilin mutanen da aka kashe a majalisar Wakilai ta ƙasa, yana kira ga shugaban Najeriya Bola Tinubu, da babban Sifeton ƴan sanda, da su yi duk mai yiyuwa wajen ganin an kamo waɗanda suka yi wannan aika-aikar tare da hukunta su, da kuma biyan diyya ga iyalan waɗanda suka rasu da kula da waɗanda suka jikkata.

“Kasancewar wannan bashi ne na farko da ake samun wasu ɓata gari na tare matafiya akan hanya da basu ji ba basu gani ba su kashe su, a don haka muna fatan wannan karon gwamnati da sauran hukumomin tsaro za su ƙaddamar da ƙwaƙƙwaran bincike don ɗaukae mataki kamar yadda dokar kasa ta tanada, “in ji Rurum”.

Ɗan majalisar ya kuma jajantawa dukkanin al’ummar jihar Kano musamman Iyalan waɗanda suka rasu, tare da addu’ar Allah ya gafarta musu yasa Jannatul Firdausi makomar su, su kuma waɗanda suka jikkata Allah ya basu lafiya.

Continue Reading

Trending