Connect with us

Manyan Labarai

An chase rawar shoki a biki wasu masoya yan shekaru 80

Published

on

An dai daura auren Dattawanne amarya Fatsima Mai shekaru 82 da Angonta Muhammadu Liti, mai shekaru 74 a ranar lahadin data gabata.

Mazauna unguwar Dorayi Amarya da Liti sun samu tagomashin abokai da yan uwa da kuma jama’ar gari.

Wakilinmu Abba Isah Muhammad ya kurda cikin taro inda ya zanta da ango kasha kamshi Muhammadu Liti, wanda yace zai shafe tsawon makonni biyu yana angwanci a dakin amaryar sa ba tare da ya leko waje ba.

Anasu bangaren abokan ango sun shaidawa wakilin namu cewar zasu yi dukkanin al’adu da suka jibanci angwanci, kama daga siyen baki zuwa raka ango da dankwaleliyar kaza ta amarci.

Babban abokin ango mai suna Sama’ila Mu’azu Adamu yace zasu yi komayya kashegarin ranar litinin domin ganin yadda angwayen suka hantse, wannan kuwa alada ce a kasar hausa.

Anata bangaren amarya Fatsima mai shekaru 82, tace yau farin cikinta daya ne dana wadda taje aikin hajji a Saudiyya.

Fatsima tace sun dade suna soyayya har tsawon watanni 8, yau kuma alkawalin Allah ya cika a wannan rana, domin shekaru 12 da kashe sardauna tayi auren farko, lokacin tana da shekaru 12 da haihuwa.

Ita dai amarya Fatsima tana da yaya 12, da jikoki da dama wanda wasu daga cikin su suka bayyana jin dadin su game da ganin ranar auren wadda suke yiwa lakabi da abokiyar su.

Wakilinmu Abba Isah Muhammad, ya ruwaito cewa an daura Auren bisa sadaki zunzurutun Kudi Har Naira Dubu Goma, yayin da a daya bangaren DJ ya saki sautin rawar shoki da azonto inda aka shakata cikin jin dadi.

Manyan Labarai

Bama goyon bayan ƙirƙiro ƴan sandan jahohi dan ba zai haifar da Ɗa mai ido ba a ƙasa – Human Rights

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Universal Declaration of Human Rights, ta ce akwai buƙatar duba na tsanaki gabanin sahale ƙirƙirar ƴan sandan jahohi, domin gujewa abinda ka je ya dawo.

Daraktan ƙungiyar a nan Kano Kwamared Umar Sani Galadanci, ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da gidan rediyon Dala FM, a yau Talata.

Galadanci, ya kuma ce duba da a mafi yawan lokuta ake samun baragurbi a harkar samar da taro, kamata ya yi a wadata jami’an tsaron da ake da su da kayan aiki na zamani, ta yadda za’a ƙara musu Gwiwa akan aikin su.

“A ɓangaren ƙungiyar mu bama goyon bayan samar da ƴan sandan jahohi, domin hakan ka iya haifar da koma baya; kuma ba zai haifar da Ɗa mai ido ba a sassan ƙasar nan, “in ji shi”.

Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa Kwamared Umar Sani Galadanci, ya ƙara da cewa akwai buƙatar gwamnatin tarayya da ta jahohi, su kula da al’ummar su tare da samar musu kayayyakin more rayuwa, dan rayuwar su ta tafi yadda ya kamata.

Continue Reading

Manyan Labarai

Mutane uku sun rasu yayin ciro Waya a cikin Masai da ceto mutum ɗaya a Kano – Hukumar Kashe Gobara 

Published

on

Hukumar kashe Gobara ta jihar Kano, ta tabbatar da mutuwar wasu mutane uku, ciki har da Uba ɗan sa, a unguwar Ƴar Gwanda da ke ƙaramar hukumar Tsanyawa a jihar Kano.

Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar kashe gobarar PFS Saminu Yusuf Abdullahi, ne ya bayyanawa gidan rediyon Dala FM, faruwar lamarin a daren jiya Lahadi.

Tunda fari dai mutum na farko mai suna Mallam Ɗan Juma mai laƙabin Black, wayar sa ce ta faɗa a cikin Masai, ya shiga domin ya cirota, sai dai gaza fitowar sa ke da wuya sauran mutane ukun suka bishi domin ceto shi lamarin da suma suka gaza fitowa.

Sauran mutane ukun akwai ɗan mutumin mai suna Ibrahim Ɗan Juma mai shekaru 35, sai na ukun mai suna Aminu T Gaye, da na huɗu mai suna Abbas Alhassan, ɗan shekara 28, amma shi an ciroshi a raye.

PSF Saminu Yusuf, ya kuma ce bayan faruwar lamarin ne jami’an su, suka ceto mutum na ƙarshe a raye, amma ukun farko basa cikin hayyacin su baki daya.

Ya ƙara da cewa tuni jami’an nasu suka miƙa mutanen a hannun jami’in hukumar ƴan Sanda, kuma babban baturen ƴan sanda da ke ƙaramar hukumar Tsanyawa a Kano mai suna SP Ibrahim Lado, inda suka kai su asibitin ƙwararru na ƙaramar hukumar Tsanyawa a Kano.

Continue Reading

Manyan Labarai

Gwamnan jihar Kano ya jagoranci ƙaddamar da fara aikin gadar sama da ƙasa ta Tal’udu

Published

on

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya jagoranci ƙaddamar da fara aikin gadar sama da ta ƙasa da za’ayi a shataletalen Tal’udu, da ke ƙaramar hukumar Gwale, domin samar wa al’ummar jihar saukin zirga-zirga a yankin.

Gwamnan yanyi wannan jawabin ne da yammacin yau Asabar yayin da yake ƙaddamar da aikin.

Haka kuma gwamnan ya ce gwamnatin Kano za ta sanya idanu wajen ganin an kammala aikin cikin ƙanƙanin lokaci, hakan ya sa yanzu haka gwamnatin ta tanadi duk wasu kayan aiki da ake buƙata domin gudanar da aikin.

Har ila yau, gwamna Abba Kabir, ya ce yanzu haka gwamnatin sa ta shirya tsaf wajen bayar da tallafi ga matasa, domin samar musu da hanyoyin sana’o’in dogaro da kai.

Wakilinmu na fadar gwamnatin Kano Umar Abdullahi Sheka ya rawaito cewa, gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya ƙara da cewa an samo kamfani mai inganci wanda zai yi aikin cikin ƙanƙanin lokaci.

Continue Reading

Trending