Manyan Labarai
Auren wuri yana kare cutar karin mahaifa-Likitoci

Likitoci a bangaren haihuwa sun bayyana cewar auren wuri yana hana kamuwa da ciwon karin mahaifa.Wani babban mata a birnin Ikko Dakta Gabriel Akilo ke bayyana hakan a wajen wani taron karawa juna sani karo na 9 daya gudana a jihar Legas ranar Alhamis data gabata.Dakta Akilo yace cutar tana kama mata ne lokacin da shekarun su suka tura batare da haihuwa akai akai zamanin budurci ba.Likitan yace binciken su ya gano cewar auren wuri, da kuma haihuwa a lokutan kuruciya yana karawa mahaifa lafiya, idan kuma girma ya fara kama su kuwa akwai bukatar su huta, a cewar sa.
Akwai bukatar mu tattauna wannan babbar matsala dake fantsama kamar wutar daji, ciwon na karin mahaifa yana yawaita a tsakanin mata ne yan shekaru 35 zuwa 45.
Ko da yake likitan yace zai yi wuya a samu yan kasa da shekaru 20 da wannan lalura, a saboda haka yake shawartar mata su rungumi auren wuri domin samun lafiyar jiki data ciki domin kawar da cutar a kasarnan.A ganin sa ba wani abune ke hana matan auren na wuri ba illa ruwan ido, da yace anan ne suke jifan gafiyar bedu wajen asarar maza nagari.Dakta Akilo ya bukaci iyaye su karfafawa yayan su mata gwiwar auren wuri domin kawar da lalurar karin mahaifa a tsakanin al’umma.Daga nan likitan ya ja hankalin mata game da magunguna da suke sha domin samun saukin cutar, gudun kaucewa rasa idanu a wajen neman gira. Yace wasu magungunan su kan illata koda, mafitsara, yayan hanji da dukkanin bangarori dake taimakawa kwaryar ciki.

Manyan Labarai
Ba za mu amince da yadda ake yawan kai wa jami’an mu hari ba a Kano – KAROTA

Hukumar kula da zirgar-zirgar ababen Hawa ta jihar Kano, KAROTA, ta ce ba za ta lamunta da yadda ake yawan kai wa jami’anta farmaki ba, na ba gaira babu dalili yayin da suke gudanar da ayyukan su.
Shugaban Hukumar KAROTA, a Kano, Injiniya Faisal Mahmud Kabir, ne ya yi wannan gargaɗin ta cikin sanarwar da kakakin hukumar Abubakar Ibrahim Sharada ya aikowa tashar Dala FM Kano, a ranar Laraba 09 ga watan Afrilun 2025.
“Hakan na zuwa ne biyo bayan wani mummunan hari da wasu mutane da ke cikin baburin Adai-daita sahu suka kai wa jami’an na mu yayin da suke tsaka da aikinsu a titin da ke dab da gidan Buhari kan hanyar zuwa Gidan Zoo, “in ji shi“.
Sanarwar ta ce, tunda farko an tsayar da wani mai baburin Adai-daita Sahu ne inda yaƙi tsayawa, sai kawai aka hango mai ɗan sahun ya naushi jami’in karotar.
Sai dai a ta bakin Shugaban kungiyar ‘Yan Adai-daita Sahu a jihar Kano, ya ce waɗannan mutane ba halattattun ‘Yan Adai-daita Sahu ba ne, sun dai fake da sana’ar su dan aikata ta’addanci.
Daga bisani dai jami’n hulɗa da jama’a na Hukumar Koratar, Abubakar Ibrahim Sharada, ya ce hukumar za ta ɗauki tsattsauran mataki akan lamarin, don kare afkuwar irin hakan a gaba.
Hukumar ta ce duk wanda ya ga faruwar wani abu da ya shafe ta, ko kuma ƙorafe-ƙorafe, zai iya kiran waɗannan lambobin domin sanar da ita, da suka haɗar da 09015709449 ko 08059689422 ko kuma 08067311520.

Manyan Labarai
Ɗan Bijilante ya rasa ransa bisa arangamar su da wasu ƴan Daba a Kano

Ƙungiyar sintirin Bijilante ta ƙasa reshen jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin kwamandan ta Ubale Barau Muhammad Badawa, ta tabbatar da rasuwar guda daga cikin jami’in ta mai suna Suraj Rabi’u mazaunin Jaba da ke ƙaramar hukumar Fagge a jihar, sakamakon arangama da ƴan Daba.
Mai magana da yawun ƙungiyar Bijilante na jihar Kano, kuma Kwamandan ta na ƙaramar hukumar Fagge, Usman Muhammad Ɗan Daji, shi ne ya bayyana hakan ta cikin wani saƙon murya da ya aikowa Dala FM Kano a ranar Lahadi.a
“Jami’in Bijilanten namu ya rasa ran nasa ne sakamakon arangama da suka yi da wasu Ƴan Daba yayin gudanar aikinsu a ranar Idin ƙaramar Sallah, inda ƴan dabar suka soke shi da Ɗanbida a Ƙirji da bayansa, wanda ya yi sanadiyar rasuwarsa, “in ji Usman”.
Ya kuma ce, an kama ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi mai suna Usman Sharif mazaunin ƙaramar hukumar Dala, kuma tuni aka miƙa shi hannun jami’an tsaro.
Usman Ɗan daji, ya kuma yi addu’ar Allah ya jiƙan jami’in nasu ya gafarta masa.

Manyan Labarai
An ga watan ƙaramar Sallah a Najeriya – Sarkin Musulmi

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na uku ya tabbatar da ganin jinjirin watan Shawwal a Najeriya, inda za a yi karamar Sallah gobe Lahadi.
Sarkin Musulmin ya bayyana hakan ne a yayin jawabin da ya gabatar a cikin daren Asabar ɗin nan, ya ce sun samu rahotannin ganin watan ne daga sassa daban-daban na ƙasar nan.
Alhaji Sa’ad Abubakar ya ce daga cikin guraren da aiko musu da ganin jinjirin watan na Shawwal akwai Zazzau, da kuma daga Sarkin Dutse, da Arugungu, da kuma Shehun Borno, da dai sauran gurare daban-daban na Najeriya.
Ya kuma yi kira ga al’ummar Musulmi da su gabatar da bikin sallar cikin kwanciyar hankali, tare da taimaka wa mabuƙata.
Tashar Dala FM Kano ta ruwaito cewa, biyo bayan sanarwar fadar mai alfarma Sarkin Musulmi, ya kasance ranar Lahadi take 1 ga watan Shawwal na shekarar 1446, wato ranar ƙaramar Sallah.

-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai4 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi5 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su