Labarai
Motsa jiki na maganin ciwon Koda- Dr. Saminu
Wani masani lafiya a bangaren aikin koda dake asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano Saminu Muhammad ya ja hankalin masu ciwon koda da su rinka bin ka’idojin da likita ya dora su akai, domin tabbatuwar lafiyar su.
Malam Saminu ya bayyana hakan yayin ne zantawarsa da gidan rediyon Dala a yau Litinin.
Ya ce “Barin fitsari ko ciwon sanyi da kuma ciwon Suga da hawan jini na daga cikin alamomin dake haddasa ciwon na koda”.
Ya kara da cewa, “Yawan motsa jiki tare da shan ruwa akai-akai da kuma kulawa da tsaftar muhalli da ta jiki, ya na taimakawa gaya wajen rage ciwon Koda”. A cewar Saminu Muhammad.
Wakiliyar mu Maryam Muhammad Usman ta rawaito cewa, malam saminu muhd na kara shawartar al’umma da su rinka ziyartar asibiti da zarar sun ji wani sauyin yanayi a jikin su.
Labarai
Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa
An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.
Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.
Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.
Hangen Dala
Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano
A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.
Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.
Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.
Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.
Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.
Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito
Labarai
Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure
Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.
Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.
Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.
Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.
-
Nishadi4 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai4 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Manyan Labarai4 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Nishadi5 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai4 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya2 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai4 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi4 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su