Connect with us

Labarai

SARAKUNAN GARGAJIYA NA JIHAR EKITI SUNYI KIRA GA AL’UMMAR JIHAR

Published

on

Sarakunan gargajiya a jihar Ekiti, sunyi kira ga al’ummar jihar da su gudanar da zaben gwamnan jihar da za’a yi a gobe Asabar cikin lumana, tare da rokon al’ummar jihar da su gujewa abin da ka iya jawo tashin hankali a yayin zaben.
Shugaban majalisar sarakunan jihar Ekiti, Oye Oba Demola Jude, ya bayana cewa,addu’a tare da soyayyar juna shine kadai zai kawo musu masalaha, a don haka suke kira ga al’ummar jihar da su yi zaben cikin lumana.
Haka shi ma sarkin Ijero Ekiti, Oba Bayo Adawale, yace mutane su sani cewa ba duka ‘yan takarar gwamnan zasu zama gwamna ba, Mutum daya ne zai ci zabe, saboda haka duk wanda ya lashe zaben a bashi goyon baya dari bisa dari.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Mataimakin babban sifeton ‘yan sandan kasar nan mai kula da ayyukan ‘yan sandan, Joshak Habila, ya bada umurnin a janye ‘yan sandan dake tsaron lafiyar manyan mutane, sanadiyar zaben gwamnan da za’a yi a jihar ta Ekiti a gobe Asabar, domin tabbatar da tsaro a ranar zaben.

Baba Suda

Hukumar tattara kudaden shiga ta Kano ta rufe wasu bankuna

Published

on

Hukumar Tattara kudaden shiga ta jahar kano ta kulle bakin Eco da Zenith dake kan titin Murtala Muhammad. Sakamakon rashin biyan haraji.

Cikakken labarin na Zuwa….

Continue Reading

Baba Suda

Kisan Makurdi:- Gwamnatin Kano za ta tura wakilai

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano tayi Allah wadai da kisan mutane biyu Yan Jihar a garin Makurdi dake Jihar Benue.

Cikin sanarwar da Daraktan Gwamnan Kano kan harkokin yada labarai Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ta ruwaito Gwamnan na Mika sakon jaje ga alummar Jihar da iyalai da ‘yan uwan wadanda abin ya rutsa dasu, Barhma Suleman da Jamilu Ahmad.

 

Kazalika Gwamnan yayi alkawarin daukar Matakin da ya dace kan batun, tare da fadin gwamnatin Kano za ta tashi wakilai har Zuwa Jihar Benue domin tabbatar da daukar Matakin da ya dace.

 

 

Continue Reading

Baba Suda

NNPP:- Kwankwaso ya sulhunta rikicin jamiyyar

Published

on

Rahotanni daga Abuja sun tabbatar da jagoran kwankwasiyya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi wani zama da Dan majalisar tarayya Mai wakiltar kananan hukumomin Rimin Gado, Tofa da Dawakin Tofa, Wato Honorable Abdulkadir Jobe, da kuma Daraktan yada labaran Gwamnan Kano Honorable Sunusi Bature Dawakin Tofa.

 

Ganawar wadda ta gudana a yammacin wannan Alhamis ta kawo karshen Jan Zaren dake faruwa tsakanin Dan majalisar da kuma Sunusi Bature.

 

A baya bayan nan dai an kai ruwa rana tsakanin su, Inda kowa ne bangare ke mayar da martani.

Abdulkadir Jobe da kuma Sunusi Bature dukkanin su mabiya jamiyyar NNPP ne tsagin kwankwasiyya.

Continue Reading

Trending