Labarai
An tallafawa mahaifiyar Yaron da a ke zargi ya sayar da waya ya siyo kayan abinci

Mazauna yankin Gaida Tsakuwa a karamar hukumar Kumbotso, sun tallafawa gidan kankanin Yaron nan da a ke zargi ya dauki wayar Salula ya sayar da ita ya siyo wa gidan su guntuwar Shinkafa danya da sinadarin dandano da danyen mai saboda yunwa da su ke fama da ita.
Kwamandan Bijilanten yanki, Shekarau Cinnaka ba ka san na gida ba ne ya tabbatar da hakan lokacin da ya ke tattaunawa da Dala FM.
Ya ce“Yanu haka mun samu ma su kishin al’umma, sun tausayawa gidan wannan yaron da buhun Shinkafa da kwalin Taliya da buhun Gawayi, sannan an dauki nauyin karatun yaran su biyu, sakamakon mahaifin su ya rasu, bayan da a ka kawo mana yaron mu ka tambaye shi, ya ce mana ya dauki wayar ne ya sayar da ita ya siyawa gidan su ‘yar wata kankanuwar Shinkafa danya da sinadirin dandano da kuma danyan man girki”. Inji Shekarau.
Kwamandan yankin kungiyar Bijilante na Gaida Tsakuwa da Kewaye, Shekarau Cinnaka ba kasan na gida ba, ya tabbatar da cewa yaron nan mazaunin yankin mai shekaru kasa da 10 da a ke zargi ya dauki wayar Salula ya siyar ya siyawa gidan su ‘yar guntuwar danyar Shinkafa da sinadirin dandano da kuma.

Baba Suda
Hukumar tattara kudaden shiga ta Kano ta rufe wasu bankuna

Hukumar Tattara kudaden shiga ta jahar kano ta kulle bakin Eco da Zenith dake kan titin Murtala Muhammad. Sakamakon rashin biyan haraji.
Cikakken labarin na Zuwa….

Baba Suda
Kisan Makurdi:- Gwamnatin Kano za ta tura wakilai

Gwamnatin Jihar Kano tayi Allah wadai da kisan mutane biyu Yan Jihar a garin Makurdi dake Jihar Benue.
Cikin sanarwar da Daraktan Gwamnan Kano kan harkokin yada labarai Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ta ruwaito Gwamnan na Mika sakon jaje ga alummar Jihar da iyalai da ‘yan uwan wadanda abin ya rutsa dasu, Barhma Suleman da Jamilu Ahmad.
Kazalika Gwamnan yayi alkawarin daukar Matakin da ya dace kan batun, tare da fadin gwamnatin Kano za ta tashi wakilai har Zuwa Jihar Benue domin tabbatar da daukar Matakin da ya dace.

Baba Suda
NNPP:- Kwankwaso ya sulhunta rikicin jamiyyar

Rahotanni daga Abuja sun tabbatar da jagoran kwankwasiyya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi wani zama da Dan majalisar tarayya Mai wakiltar kananan hukumomin Rimin Gado, Tofa da Dawakin Tofa, Wato Honorable Abdulkadir Jobe, da kuma Daraktan yada labaran Gwamnan Kano Honorable Sunusi Bature Dawakin Tofa.
Ganawar wadda ta gudana a yammacin wannan Alhamis ta kawo karshen Jan Zaren dake faruwa tsakanin Dan majalisar da kuma Sunusi Bature.
A baya bayan nan dai an kai ruwa rana tsakanin su, Inda kowa ne bangare ke mayar da martani.
Abdulkadir Jobe da kuma Sunusi Bature dukkanin su mabiya jamiyyar NNPP ne tsagin kwankwasiyya.

-
Nishadi6 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai5 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi6 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi6 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su