Labarai
Tuƙin Ganganci: Mai mota ya ture mai Adaidaita Sahu daga gadar sama
Wani mai mota da ke zargi ya ture wani mai babur din Adaidaita Sahu daga gadar sama ta titin By-Pass a yankin karamar hukumar Kumbotso, lamarin da ya jikkata direban babur din.
Shaidun gani da ido sun shaidawa wakilin mu Nasiru Khalid Abubakar, cewa mai motar ya hankado mai babur din daga saman gadar, lamarin da babur din ya tuntsuro har zuwa kasa.
Tuni a ka garzaya da mai Adaidaita Sahun zuwa asibiti mafi kusa, duba da yadda ya ji munanan raunuka a kansa, dama wasu sassan jikinsa.

Baba Suda
Hukumar tattara kudaden shiga ta Kano ta rufe wasu bankuna
Hukumar Tattara kudaden shiga ta jahar kano ta kulle bakin Eco da Zenith dake kan titin Murtala Muhammad. Sakamakon rashin biyan haraji.

Cikakken labarin na Zuwa….

Baba Suda
Kisan Makurdi:- Gwamnatin Kano za ta tura wakilai
Gwamnatin Jihar Kano tayi Allah wadai da kisan mutane biyu Yan Jihar a garin Makurdi dake Jihar Benue.
Cikin sanarwar da Daraktan Gwamnan Kano kan harkokin yada labarai Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ta ruwaito Gwamnan na Mika sakon jaje ga alummar Jihar da iyalai da ‘yan uwan wadanda abin ya rutsa dasu, Barhma Suleman da Jamilu Ahmad.
Kazalika Gwamnan yayi alkawarin daukar Matakin da ya dace kan batun, tare da fadin gwamnatin Kano za ta tashi wakilai har Zuwa Jihar Benue domin tabbatar da daukar Matakin da ya dace.

Baba Suda
NNPP:- Kwankwaso ya sulhunta rikicin jamiyyar
Rahotanni daga Abuja sun tabbatar da jagoran kwankwasiyya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi wani zama da Dan majalisar tarayya Mai wakiltar kananan hukumomin Rimin Gado, Tofa da Dawakin Tofa, Wato Honorable Abdulkadir Jobe, da kuma Daraktan yada labaran Gwamnan Kano Honorable Sunusi Bature Dawakin Tofa.
Ganawar wadda ta gudana a yammacin wannan Alhamis ta kawo karshen Jan Zaren dake faruwa tsakanin Dan majalisar da kuma Sunusi Bature.
A baya bayan nan dai an kai ruwa rana tsakanin su, Inda kowa ne bangare ke mayar da martani.
Abdulkadir Jobe da kuma Sunusi Bature dukkanin su mabiya jamiyyar NNPP ne tsagin kwankwasiyya.

-
Nishadi6 years agoIna neman mijin aure – Rayya
-
Labarai5 years agoHamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi6 years agoMansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai6 years agoKAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai6 years agoAuren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years agoRahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai6 years agoSabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi6 years agoAn gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
