Connect with us

Labarai

Kotu ta ki amincewa da bukatun tsagin Ganduje

Published

on

Wata babbar kotun birnin tarayya Abuja, ta ki amincewa da bukatar da wasu ‘yan jam’iyyar APC na jihar Kano masu biyayya ga gwamna Abdullahi Ganduje su ka yi na a yi watsi da hukuncin da ya tabbatar da zaman taron jam’iyyar da wani bangare ya yi.

Kotun da ke karkashin mai shari’a, Hamza Mu’azu ta kuma ki amincewa da hukuncin da a ka shigar na dakatar da aiwatar da hukuncin har sai an yanke hukuncin daukaka kara a kotun daukaka kara.

Kotun dai a ranar 30 ga watan Nuwamba, 2021, ta tabbatar da zaben shugabannanin kananan hukumomi tsagin, Sanata Ibrahim Shekarau.

Kotun dai ta ki amincewa da matakin farko da ke biyayya ga Gwamna Ganduje.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Labarai

Rahoto: Dokar hana shan shisha ta fara aiki gadan-gadan a Kano – Hisba

Published

on

Hukumar Hisba ta jihar Kano ta kai simamen shagunan da ake sayar da Shisha a kan titin Bompai da ke jihar Kano, inda ta samu nasarar kama dillalan Shishar, domin tabbatar da dokar hana sha da siyar da ita.

A zantawar daya daga cikin masu shagunan sayar da Shisha da wakilin mu na ‘yan Zazu, Ibrahim Abdullahi Soron Dinki, ya bayyana cewar, ya yi tunanin dokar hana shan Shisha ta tsaya kan masu wuraren shan Shisha ba masu sayarwa ba.

Mu na da cikakken rahoton a muryar da ke kasa.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Shekaru 10 ina sarrafa Turoso amma ko ciwon kai ban taba yi ba – Mai Turoso

Published

on

Wani magidanci mai sana’ar sarrafa Turoso a yankin Kududdufawa ya ce, sama da shekaru goma ya na aikin sarrafa Turoso, amma ko ciwon kai bai taba yi ba.

Malam Isah Musa Katsinawa mazunin karamar hukumar Ungogo a jihar Kano, ya bayyana hakan ne, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Yusuf Nadabo Isma’il.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Gobara ta lakume ran mutane 3 ciki harda dattijuwa

Published

on

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kano, ta kai tallafi wani gida da aka samu iftila’in gobara, wanda ta yi sanadiyar rasa mutane Uku  a unguwar Gama A, da ke karamar hukumar Nasarawa.

Wakilin mu na ‘yan zazu, Abba Isah Muhammad, ya rawaito cewar, hukumar karkashin shugabanta Salihu Aliyu Jili, ta kuma kai tallafi gidan iyayen Hanifa, dalibar da aka yi zargin malaminta ya kashe ta.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Trending