Connect with us

Labarai

Mai gabatar da shiri a Talabijin ta shafe kwanaki 322 ba ta fita daga gida ba saboda tsoron Corona

Published

on

Shahararriyar mai gabatar da shirye-shirye a gidan talabijin na kasar Amurka, Oprah Winfrey, ta bayyana cewa, ta keɓe kanta a cikin gidanta, saboda tsoron kamuwa da COVID 19, har na tsawon kwanaki 322.

Yayin da take haɓaka sabon shirinta mai suna The Color of Care a cikin wata hira da jaridar Los Angeles Times, mai yada shirye-shiryen talabijin ta ce, a zahiri ba ta bar gidanta ba kusan shekara guda.

Oprah Winfrey mai shekaru 68 ta kuma ce, “Ban bar gida ba tsawon kwanaki 322, a zahiri ban bar gidana ba,” in ji ta ga tashar yayin da take bayyana cewa abin da ya fi ba ta mamaki game da zama cikin keɓe “shine yadda na sami damar daidaitawa da keɓe da rashin kasancewa a kusa. sauran mutane.”

Ta tuna, “Na tuna wani batu Gayle King ya ce, ‘Ba ku kawai kewar kasancewa tare da wasu ba?’ Na tafi, ‘ba da gaske ba.’

Winfrey ya bayyana cewa: “Kuma ina tsammanin saboda kowace rana, ina cikin masu sauraron mutane 350 sau biyu a rana (lokacin da ake nuna Oprah Winfrey Show), don haka na yi ta girgiza hannu da hotuna, da kuma mai da hankali sosai, kuma bayyanar da kasancewa kusa da mutane da yawa.”

Ta kara da cewa “Na iya zama da kaina ta hanyar da ban samu damar yin shekaru da yawa ba, saboda yawanci ko da na dauki lokaci don kaina, ina tunanin abin da zai biyo baya,” in ji ta. .

Labarai

Mu taimaka wa masu ƙaramin ƙarfi domin rage musu raɗaɗin rayuwa – Ambada Muhammad

Published

on

Shugaban ƙungiyar mu haɗa zumunci ta KHZ Foundation dake nan Kano Ambasada Dakta Muhammad Abdulsalam, ya ce, taimakawa masu ƙaramin ƙarfi musamman a wannan lokaci na watan Azumin Ramadana, zai taimaka musu wajen rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Ambasada Muhammad Abdulsalam ya bayyana hakan ne a yayin taron baiwa iyayen marayu da masu ƙaramin ƙarfi tallafin kayan abinci a ofishin kungiyar yau Litinin, da kuma basu a wasu unguwanni da suka haɗar da Tukuntawa da Sabuwar Gandu, Tinshama da dai sauransu.

Ya kuma ce, kamata yayi al’umma su ƙara himma wajen shiga makamancin ƙungiyar su domin baiwa al’umma gudunmawar da ta kamata, ta hanyoyi daban-daban, domin cire musu wata damuwa da ta damesu a rayuwa.

“Zamu fitar da ɗaurarru masu ƙananan tara a wasu gidjen ajiya da gyaran hali domin fitar da su daga halin rayuwar da suke ciki na jarrabta da suka tsinci kan su”. In ji Ambasada Muhammad.

Da yake nasa jawabin malami a kwalejin ilmin tarayya ta FCE dake nan Kano Mallam Ibrahim Muhammad Gandu, gargaɗar iyayen marayun da sukaci gajiyar tallafin yayi, da su yi amfani da kayayyakin abincin ta hanyar da ta dace Mai-makon siyar da kayan a ƙasƙance da ake zargin wasu suna yi a wasu lokutan.

Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewar, iyayen marayu da masu ƙaramin ƙarfi da dama ne suka rinƙa bayyana farin cikinsu, bisa basu kayan abincin da akayi, wanda suka haɗar da Shinkafa, Gero Taliya Man girki da sai sauransu, haɗi da Naira dubu ɗaya kuɗin Mota ga kowannen su.

Continue Reading

Labarai

Ɗaurarru sama da dubu 1 aka duba lafiyar su a Kano

Published

on

Ɗaurarru sama da dubu ɗaya ne dake zaune a gidajen gyaran hali na goron Dutse da Kurmawa a jihar Kano, suka amfana da ganin likitoci daban-daban tare da ba su magani kyauta.

Yayin wani aikin sa kai da nufin neman lada a wajan Allah da tawagar ƙungiyar likitoci musulmi suka yi, ƙarƙashin jagarancin shugaban kwanitin gudanar da aikin Dr. Sule Abdullahi Gaya.

Har ma shugaban ƙungiyar na jihar Kano, Dr. Muhammad Auwal ya ce, suna yin aikin ne domin taimakawa marasa ƙarfi a wurare daban-daban, tare da basu kayan abinci da ruwa, da makamantan su.

A jawaban su daban-daban Dr. Anas Ibrahim Yahaya Bichi da Dr. Muhammad Lawan Adamu waɗanda suna cikin likitocin da suka duba marasa lafiya da dama cewa suka yi, a tafiyar ta su babu irin likitan da babu, don haka kowacce irin cuta suka ci karo da ita sun tanadi maganin ta.

Daga bisani mai kula da gidan gyaran halin na Kurmawa DC Mu’azu Tukur wanda ya yi jawabi a madadin shugaban hukumar ya nuna godiya da jin dadin su kan aikin da kungiyar likitoci musulmi suka yi ga daurarrun.

Continue Reading

Labarai

Tallafawa masu ƙaramin ƙarfi na rage musu raɗaɗin rayuwa – Kwamared Galadanchi

Published

on

Shugaban ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Universal Declaration of Human Right Network dake nan Kano Kwamared Umar Sani Galadanchi, ya ce tallafawa masu ƙaramin ƙarfi gida hanya da na Asibiti yakan tallafa musu wajen rage musu wani raɗaɗin rayuwa da yake damunsu.

Kwamared Umar Galadanchi ya bayyana hakan ne a yayin da tawagar su ta sauke kayan shan ruwa ga marasa lafiya a wasu ɓangare na Asibitin Murtala dake nan Kano a ranar Lahadi.

Yana mai cewa, sun kaiwa marasa lafiyar kayan shan ruwan ne domin rage musu wata damuwa da take damunsu na yau da kullum.

“Yana daga cikin wajibcin aikace-aikacen ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam su tallafawa masu ƙaramin ƙarfi da lafiya, karfi da kuma aljihu domin ragewa mutane wata damuwa da take damun su”. Inji Umar Galadanchi.

Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa Umar Sani Galadanchi, ya kuma yi kira ga masu zuciya da su ƙara taimakawa al’umma musamman ma a wannan lokaci na Azumin watan Ramadan da ake ciki, da ake matuƙar buƙatar Mai-makon kashe dukiyoyin ta hanyar da basu da ce ba.

Continue Reading

Trending