Connect with us

Labarai

Jirgin dakon kaya na farko ya fara sauka a tashar ruwan Lekki – Buhari

Published

on

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya taya ma’aikatar sufuri ta tarayya da hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta kasa, murna kan nasarar da aka samu na jigilar jirgin ruwa na farko a tashar ruwan Lekki Deep Sea da ke jihar Legas.

Jirgin mai suna ZHEN HUA 28, ya kai jirgin ruwa guda uku zuwa teku da wasu kugiya guda 10,  wadanda za su taimaka wajen fitar da kayayyaki daga tasoshin zuwa gaci.

Shugaban ya bayyana ra’ayinsa ne a wata sanarwa da mai magana da yawunsa Femi Adesina ya fitar ranar Asabar a Abuja.

Ya kuma taya dukkan masu ruwa da tsaki a harkar ruwa murnar wannan gagarumin aiki.

A cewarsa, an yanke shawarar ne da nufin samar da guraben ayyukan yi masu tarin yawa, zuba jarin kasashen waje da kuma saukaka harkokin kasuwanci.

Ya yabawa ma’aikata da masu gudanarwa a bangaren ruwa na kasar da suke aiki ba dare ba rana don ganin an fara gudanar da aikin tashar ruwan Lekki kafin karshen shekara.

Shugaban ya tabbatar musu da kudirinsa na ci gaba da saka hannun jari a wadannan sabbin kadarorin.

A cewar Buhari, albarkatun ruwa da na ruwa na kasar na da matukar muhimmanci ga rayuwar ‘yan Najeriya kuma gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen samun nasarar cin moriyar wannan fanni.

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Labarai

Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.

Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Trending