Connect with us

Manyan Labarai

Tinubu da Shettima za su karawa Buhari nasarori a shekaru 7 – Kungiyar Gwamnonin APC

Published

on

Gwamnonin jam’iyyar APC, sun ziyarci shugaban kasa Muhammadu Buhari a garin Daura na jihar Katsina.

Gwamnonin bayan isar su gidan shugaban sun shiga ganawar sirri.

Gwamnonin APC bayan ganawarsu da Buhari, sun yabawa dan takarar shugaban kasa, Bola Tinubu kan zaben tsohon gwamnan jihar Borno, Kassim Shettima a matsayin abokin takararsa a zaben 2023.

Gwamnonin da suka ziyarci shugaba Buhari a ranar Litinin sun hada da, Aminu Masari na jihar Katsina, Abdullahi Ganduje na jihar Kano, Atiku Bagudu na jihar Kebbi, Abubakar Bello na jihar Neja, Hope Uzodimma na jihar Imo, Kayode Fayemi na jihar Ekiti, Simon Lalong na jihar Filato. Jiha da Abdullahi Sule na jihar Nasarawa.

Gwamnan jihar Kebbi, Bagudu, yayin da yake jawabi bayan taron, ya ce, shugabancin Tinubu da Shettima zai karawa shugaba Buhari nasarori a cikin shekaru bakwai da suka gabata.

Ya kuma bayyana cewa, jam’iyya mai mulki na aiki tukuru domin ganin ta lashe zaben gwamna da ke tafe a jihar Osun.

Gwamna Uzodinma a nasa bangaren ya bayyana zaben Shettima a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar a matsayin shawarar gamayya.

Gwamnan jihar Imo ya ci gaba da cewa, gwamnonin APC ashirin da biyu za su kai jihohin su a zaben 2023 mai zuwa.

Manyan Labarai

Shekaru 63 na Nigeria:- Jawabin Gwamnan Kano

Published

on

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya buƙaci shugabanni da saura al’umma da suyi koyi da tsaffin shugabannin da suka gabata wajen kawowa ƙasar nan ci gaba da zaman lafiya musamman a irin wannan lokaci.

 

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan ne a yau yayin da yake jawabi kan cikar ƙasar nan shekara 63 da samun kyancin kai daga hannun turawan mulkin mallaka.

 

Gwamna Abba ya kuma ce la’akari da yadda ake tunawa da tsaffin shugabanni wajen ciyar da ƙasar nan gaba ya kamata su shugabannin yanzu suyi koyi da su.

 

 

Ka zalika ya ƙara da cewa ya kamata shugaban ni su tabbata sun yiwa al’umma abin da suke buƙata domin tabbatar adalci.

 

Gwamnatin tace zata ci gaba da gudanar da aikin ta kamar yadda ta tsara domin ciyar da Kano gaba.

Continue Reading

Hangen Dala

Hukuncin Kaduna :- PDP za ta daukaka kara

Published

on

Jam’iyyar PDP reshen jihar Kaduna ta yi watsi da hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben gwamna da ta tabbatar da zaben Gwamna Uba Sani na jam’iyyar APC, inda ta ce za ta garzaya kotun daukaka kara.

Alberah Catoh, Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar PDP ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a ranar Juma’a a Kaduna.

Catoh ya ce, wani nazari da lauyan PDP ya yi ya nuna cewa hukuncin bai cika wasu ka’idoji na tabbatar adalci ba.

Martanin ya zo ne sa’o’i bayan kotun da ke zamanta a Kaduna ta amince da nasarar zaben Sani.

Ya kara da cewa hukuncin bai dace da wasu dokoki da ka’idojin zabe ba.

Sanarwar ta kara da cewa, “Saboda haka jam’iyyar ta umurci lauyoyinta da su daukaka kara kan hukuncin da aka yanke a kotun daukaka kara da ke Abuja a cikin wa’adin da doka ta kayyade.”

Catoh ya kuma bukaci magoya bayan jam’iyyar PDP a fadin jihar da su kwantar da hankalinsu tare da nuna kwarin gwiwarsu kan lamarin.

Continue Reading

Hangen Dala

Abba ya biyawa Daliban Kano kudin makaranta

Published

on

Abba Kabir ya biya kuɗin makarantar ɗaliban Jami’ar Bayero

 

Gwamnatin jihar Kano ta ce, ta biya kuɗin makarantar ɗaliban Jami’ar Bayero, waɗanda ba su samu damar biya ba, kimanin Naira Miliyan ɗari bakwai.

 

Sakataren hukumar bayar da tallafin ilimi ta jihar Kano, Hon. Kabir Getso Haruna ne, ya bayyana hakan a ranar Talata.

 

Yana mai cewa, “Yanzu haka Gwamnatin Kano, ta biya wa ɗalibai ƴan asalin jihar, dubu bakwai kuɗin makarantar”.

 

Ya kuma ce, “Daga yau Talata, dukkan ɗaliban, su tafi Jami’ar Bayero, tsangayoyin su, domin ƙarasa rijista na shekarar 2023, su ci gaba da karatu”. Inji Hon. Kabir Getso.

Continue Reading

Trending