Connect with us

Labarai

Rahoto: Jihar Kano ce a kan gaba wajen yin rijistar katin zabe – INEC

Published

on

Hukumat zabe ta kasa reshen jihar Kano INEC ta ce, al’ummar jihar Kano sun bayar da hadin kai wajen fita domin yin rijistar katin Zabe.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Adam Ahmad Maulud, ya bayyana hakan, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu Yusuf Nadabo Isma’il, a dakin taro na Sani Abacha da ke jihar Kano.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Baba Suda

NNPP:- Kwankwaso ya sulhunta rikicin jamiyyar

Published

on

Rahotanni daga Abuja sun tabbatar da jagoran kwankwasiyya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi wani zama da Dan majalisar tarayya Mai wakiltar kananan hukumomin Rimin Gado, Tofa da Dawakin Tofa, Wato Honorable Abdulkadir Jobe, da kuma Daraktan yada labaran Gwamnan Kano Honorable Sunusi Bature Dawakin Tofa.

 

Ganawar wadda ta gudana a yammacin wannan Alhamis ta kawo karshen Jan Zaren dake faruwa tsakanin Dan majalisar da kuma Sunusi Bature.

 

A baya bayan nan dai an kai ruwa rana tsakanin su, Inda kowa ne bangare ke mayar da martani.

Abdulkadir Jobe da kuma Sunusi Bature dukkanin su mabiya jamiyyar NNPP ne tsagin kwankwasiyya.

Continue Reading

Labarai

Real Madrid ta kaddamar da Alexander

Published

on

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta ƙaddamar da ɗan wasa Trent Alexander Arnold a yau a matsayin ɗan wasan ta

Inda shugaban ƙungiyar Flerontino Perez yace yau suna matuƙar Farin ciki kasancewar sun mallaki babban ɗan wasan baya a duniya.

 

Shima ɗan Wasa Arnold ya bayyana cewa yana cikin farin ciki kuma mafarkin sa ya cika na zama ɗan Wasan Madrid a yau.

Continue Reading

Daurin Boye

Zan shiga kawancen ‘yan jamiyyar hamayya – tsohon Minista

Published

on

Tsohon ministan sufurin Najeriya, Rotimi Amaechi ya ce a shirye yake don shiga ƙawancen ƴan jamiyyar hamayya domin ƙalubalantar Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027

A wata hira da BBC, tsohon gwamnan na jihar Rivers ya ce suna ƙoƙarin samar da haɗakar siyasar da za ta samar da sauyi a ƙasar.

Amaechi wanda ɗan jam’iyyar APC ne  ya nuna damuwa kan abin da ya ƙira halin ƙuncin rayuwa da ƙasar ke ciki.

Amaechi ya ce bai cire tsammanin yin takarar shugaban ƙasa ba, illa lokaci ne kawai zai tantance.

Continue Reading

Trending