Connect with us

Ƙasashen Ƙetare

Rasha da Ukraine sun cimma yarjejeniya a kan toshe tan miliyan 20 na Hatsi

Published

on

Kasashen Rasha da Ukraine sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya a birnin Istanbul a ranar Juma’a, domin toshe sama da ton miliyan 20 na hatsi da ya makale a tashar ruwan tekun Black Sea da ke Ukraine.

Yarjejeniyar dai na da nufin rage hauhawar farashin hatsi da kuma rage matsalar yunwa a duniya, inji rahoton jaridar New York Times.

Wannan dai na zuwa ne bayan shafe watanni ana tattaunawa tsakanin kasashen biyu da ke rikici da juna, wadda aka kulla tare da taimakon Majalisar Dinkin Duniya da Turkiyya.

Manyan jami’an Majalisar Dinkin Duniya sun ce, jigilar hatsi na farko daga Odesa da tashoshin jiragen ruwa da ke makwabtaka da ita ya rage makwanni kacal, kuma za a gaggauta kawo tan miliyan biyar na hatsin Ukraine da sauran kayayyakin abinci zuwa kasuwannin duniya a kowane wata.

Ci gaban zai kuma ba da damar ajiya a cikin silos na Ukraine don sabbin hatsi da aka girbe, in ji jami’ai.

Ku shiga ku karanta wannan: Neman Sulhu: Rasha da Ukraine sun gana a Turkiyya

Sakatare-janar na Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres, ya ce, a taron rattaba hannu kan yarjejeniyar a Istanbul ranar Juma’a, “Wannan yarjejeniyar ba ta zo cikin sauki ba,” yana mai cewa yarjejeniyar a matsayin “tashin ruwa a tekun Black Sea.”

Sai dai ya yabawa kasashen Ukraine da Rasha da kuma Turkiyya bisa hadin kan da suka yi wajen ganin an cimma wannan nasara.

Ƙasashen Ƙetare

Sojoji Sun yi juyin Mulki a Gabon

Published

on

Sojoji sun bayyana a gidan talabijin na kasar Gabon tare da sanar da karbi mulki.

Sun ce sun soke sakamakon zaben da ka gudanar ranar Asabar, inda aka ayyana shugaba Ali Bongo a matsayin wanda ya lashe zaben.

Hukumar zaben ta ce Mr Bongo ya samu nasara ne da kasa da kashi biyu bisa uku na kuri’un da aka kada a zaben da ‘yan adawa suka ce an tafka magudi.

Sun Kuma ce Hambarar da shi zai kawo karshen mulkin shekaru 53 da iyalan gidansu ke yi a Gabon.

Sojoji 12 ne suka bayyana a gidan talabijin dake sanar da soke sakamakon zaben tare da rusa dukkan hukumomin kasar.

Daya daga cikin sojojin ya fada a tashar talabijin ta Gabon 24 cewa, “Mun yanke shawarar kare zaman lafiya ta hanyar kawo karshen mulkin da ake yi a yanzu.”

Mr Bongo ya hau karagar mulki lokacin da mahaifinsa Omar ya rasu a shekara ta 2009.

Continue Reading

Ƙasashen Ƙetare

Sojoji sunyi juyin Mulki a jamhuriyar Nijar

Published

on

Rahotanni daga jamhuriyar Nijar na cewa Sojojin Kasar sun yi juyin Mulki, tare da sanar da kawo karshen mulkin shugaba Muhammad Bazum.

Cikin sanarwar da suka bayar a gidan telebijin din Kasar, jagoran tawagar sojojin Kanal Amadu Abdramane yace “mun kawo karshen mulkin shugaba Muhammad Bazum tare da karbe dukkanin Wani Iko”.

Sojojin dai sun bayar da dalilin halin rashin tabbas da Kuma Matsin tattalin arziki a kasar.

Tuni dai sojojin suka garkame dukkanin iyakokin Kasar tare da Sanya dokar takaita zirga zirga daga karfe 10 na dare zuwa 6 na safe.

Tun a safiyar laraba ne dai aka wayi gari da fara wancan yunkuri, Wanda yanzu haka ta tabbata, Kasar Nijar na hannun sojoji, Wanda shi ne Karo na hudu ana gudanar da juyin mulkin a jamhuriyar Nijar.

Continue Reading

Ƙasashen Ƙetare

An tsaurara tsaro a fadar shugaban Kasar Nijar

Published

on

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar, na nuni da cewa dakarun da ke gadin fadar shugaban ƙasa sun rufe duk wata hanyar shiga fadar a wani lamari da ba a kai ga ganowa ba.

Sai dai rahotanni na cewa yanzu haka wasu daga cikin tsofaffin shugabannin ƙasar ta Nijar na tattaunawa da sojojin domin sasanta lamarin.

Karin bayani nan tafe….

Continue Reading

Trending