Connect with us

Labarai

Inganta tsarin kasa da kasa zai inganta harkokin lafiya – Atiku

Published

on

Dan takarar shugaban kasa a Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya shawarci hukumar asibitin Nizamiye da su ingantaccen tsarin kasa da kasa bawai kawai iya kayan aiki ba.

Atiku ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi ayarin hukumar gudanarwar rukunin First Surat Group, karkashin manajan daraktan, Yeser Ovenc, inda suka ziyarce shi a gidan sa na Asokoro dake Abuja jiya Juma’a.

Sanarwar da mai taimaka masa na musamman a harkokin yada labarai, Abdulrasheed Shehu ya sanyawa hannu, Mr Servet Gulerman, ya godewa Wazirin Adamawa, saboda samun lokacin karbar tawagar ta su, inda ya ce, sun je ne musamman domin taya shi murnar lashe zaben fitar da gwani na PDP tare da yi masa fatan nasara a babban zabe na badi.

Haka kuma, sun godewa tsohon mataimakin shugaban kasar ta Najeriya saboda irin taimako da goyon bayan da ya rika bawa kamfanin a baya. Inda ya ce, a matsayin su na wakilan al’ummar Turkawa a Najeriya sun kaiwa Wazirin na Adamawa ziyarar ban girma, yana mai cewa, za su ci gaba da zuba hannayen jari da ayyuka da za su amfani kasashen biyu domin kyautata alakar su.

Ya ce, “Irin nasarar da suka samu da fadada kwarewa a Asibitin a fannin tiyata da ta shafi zuciya da sauran cututtukan zuciya da nasara Kashi 99 cikin dari, zai taimaka mutuka Wajen rage zuwa Asibitin kasashen Waje inda aka mori Asibitin yadda ya dace”.

Labarai

NAHCON ta sanya ranar fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana zuwa Saudiyya

Published

on

Yanzu haka hukumar Aikin Hajji ta ƙasa NAHCON, ta 15 ga watan nan na Mayun 2024, a matsayin ranar da za’a fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana, zuwa ƙasa mai tsarki.

Bayanin hakan ya fito ne ta bakin shugaban hukumar ta NAHCON, Jalal Ahmad Arabi, a wajen taron masu ruwa da tsaki kan aikin Hajji da Umrah, da ya gudana yau Alhamis birnin tarayya Abuja.

“Maniyyata kimanin 65,500 ne za su sauke Farali daga ƙasar nan a ƙasa mai tsarki; za su shafe aƙalla kwanaki huɗu domin yin ziyara a Madina kafin fara aikin Hajji, “in ji Arabi”.

Daga bisani shugaban hukumar aikin hajjin Jalal Ahmad Arabi, ya kuma bayyana cewa za ayi jigilar maniyyata aikin hajjin ne daga cibiyoyi 10 a faɗi ƙasar nan.

Continue Reading

Labarai

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba, 1 ga watan Mayun 2024, a matsayin ranar hutu, domin bikin ranar ma’aikata na wannan shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

Olubunmi, ya kuma sake nanata buƙatar ganin ma’aikata sun jajirce da yin aiki yadda ya kamata a dukkanib matakai daban-daban.

Continue Reading

Labarai

Wahalar Fetur ta haifar mana da koma baya a sana’ar mu – Mai Motar Haya

Published

on

Wani mai sana’ar tuƙin motar Haya, da kuma lodin fasinjoji mai suna Kabiru Muhammad, mazaunin ƙaramar hukumar Munjibir, ya ce ƙarancin motocin Haya da ake samu a yanzu, yana da alaƙa da wahalar man Fetur da ake fuskanta a sassan Najeriya.

A zantawar mutumin da wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il, ta cikin shirin rahotanni daga ƴan Zazu na yau Talata, ya ce a baya har motoci hamsin suke yiwa lodin fasinjoji su tashi, amma a yanzu Mota ɗaya suke iya cikawa sakamakon ƙarancin Fetur da ake fama da shi.

Ya kuma ce ƙaranci tare da tsadar man fetur ɗin da ake fama da shi, sun haddasa musu koma baya a sana’ar su, baya ga batun kuma matsalar da suke fuskanta da fasinjoji wajen biyan kuɗin Mota.

Wakiliyarmu da ta bibiyi shirin na ƴan Zazu Ummi Bala Ahmad ta rawaito cewa, matuƙin motar Kabiru Muhammad, ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jahohi, da su yi abinda ya kamata dan ganin farashin man Fetur ɗin ya sauka, domin al’umma su samun sauƙi.

Continue Reading

Trending