Manyan Labarai
Kaso 40 na matasa ne idan na samu dama – Atiku

Dan takarar shugabancin ƙasa na Jam’iyyar PDP a zaben 2023, kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bawa matasan Najeriya tabbacin barin kyakkyawan tarihi a gare su, idan aka bashi damar jagorantar al’ummar kasar.
Mataimaki na Musamman ga Atiku Abubakar kan kafafen yada labarai, Abdulrasheed Shehu, ya sanya wa hannu, ya ce, Atiku Abubakar ya bada wannan tabbaci ne a ranar Laraba 3 ga watan Agusta, lokacin da ya karbi bakuncin tawagar shugabannin PDP sabon karni, karkashin jagorancin babban daraktan ta Audu Mahmud a gidan sa dake Abuja.
Atiku ya sake jaddada aniyar sa, kamar yadda ta ke kunshe cikin kundin manufofin sa, na bawa matasa dama a gwamnatin sa ta hanyar ware musu kaso 40, inda kuma ya ce, zai yi sauye-sauyen da suka kamata, domin bada dama ga mata da matasa.
Wazirin Adamawa ya kara da cewa, a gwamnatin PDP ne kawai aka aiwatar da tsarin nan na kebewa mata kaso 35, inda ya ce, APC ba ta taba girmama wannan yarjejeniya ba.
Ya kuma koka game da halin da matasa suka sami kansu, inda ya yi alkawarin daidaita al’amuran. A saboda haka, ya ce, ilimi zai zamo babban ginshikin gwamnatin sa, domin bunkasa rayuwar matasa da habaka dimukuradiyya. Ya bayyana takaici kan yadda APC ta wargaza tsarin da gwamnatin PDP ta shimfida a baya.
Yayin da yake tabbatar da muhimmancin matasa Wajen Gina kasa, Dan Takarar na PDP ya jaddada cewar, zai yi aiki da bukatun zamani, tare da gudanar da gwamnati mai tafiya tare da kowa mai la’akari da banbance-banbancen dake tsakanin mu.
A nasa jawabin, jagoran ayarin, Audu Mahmud ya ce, Atiku Abubakar wata mabubbuga ce, ta karfafa gwiwa da kyakkyawan tunani ga matasan kasar nan, inda ya bayyana yakinin da yake da shi na kwarewar Atiku domin magance matsalolin tattalin arziki da matsalolin siyasa domin amfanin dukkan yan Najeriya.

Manyan Labarai
Ɗan Bijilante ya rasa ransa bisa arangamar su da wasu ƴan Daba a Kano

Ƙungiyar sintirin Bijilante ta ƙasa reshen jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin kwamandan ta Ubale Barau Muhammad Badawa, ta tabbatar da rasuwar guda daga cikin jami’in ta mai suna Suraj Rabi’u mazaunin Jaba da ke ƙaramar hukumar Fagge a jihar, sakamakon arangama da ƴan Daba.
Mai magana da yawun ƙungiyar Bijilante na jihar Kano, kuma Kwamandan ta na ƙaramar hukumar Fagge, Usman Muhammad Ɗan Daji, shi ne ya bayyana hakan ta cikin wani saƙon murya da ya aikowa Dala FM Kano a ranar Lahadi.a
“Jami’in Bijilanten namu ya rasa ran nasa ne sakamakon arangama da suka yi da wasu Ƴan Daba yayin gudanar aikinsu a ranar Idin ƙaramar Sallah, inda ƴan dabar suka soke shi da Ɗanbida a Ƙirji da bayansa, wanda ya yi sanadiyar rasuwarsa, “in ji Usman”.
Ya kuma ce, an kama ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi mai suna Usman Sharif mazaunin ƙaramar hukumar Dala, kuma tuni aka miƙa shi hannun jami’an tsaro.
Usman Ɗan daji, ya kuma yi addu’ar Allah ya jiƙan jami’in nasu ya gafarta masa.
Manyan Labarai
An ga watan ƙaramar Sallah a Najeriya – Sarkin Musulmi

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na uku ya tabbatar da ganin jinjirin watan Shawwal a Najeriya, inda za a yi karamar Sallah gobe Lahadi.
Sarkin Musulmin ya bayyana hakan ne a yayin jawabin da ya gabatar a cikin daren Asabar ɗin nan, ya ce sun samu rahotannin ganin watan ne daga sassa daban-daban na ƙasar nan.
Alhaji Sa’ad Abubakar ya ce daga cikin guraren da aiko musu da ganin jinjirin watan na Shawwal akwai Zazzau, da kuma daga Sarkin Dutse, da Arugungu, da kuma Shehun Borno, da dai sauran gurare daban-daban na Najeriya.
Ya kuma yi kira ga al’ummar Musulmi da su gabatar da bikin sallar cikin kwanciyar hankali, tare da taimaka wa mabuƙata.
Tashar Dala FM Kano ta ruwaito cewa, biyo bayan sanarwar fadar mai alfarma Sarkin Musulmi, ya kasance ranar Lahadi take 1 ga watan Shawwal na shekarar 1446, wato ranar ƙaramar Sallah.
Manyan Labarai
Shugaba Tinubu da Sifeton Ƴan Sanda ku bi wa mutanen mu da aka yi wa kisan gilla hakƙin su – Rt. Hon. Rurum

Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Rabo, Kibiya da Bunkure, Kabiru Alhassan Rurum, ya bayyana kaɗuwar sa bisa kisan gillan da aka yi wa wasu Mafarauta su kusan 16, a garin Uromi da ke jihar Edo, a lokacin da suke hanyar su ta komawa Kano daga jihar Rivers.
Honarable Kabiru Rurum, ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da aka aikowa Dala FM Kano a ranar Asabar, ya ce daga cikin mutanen da aka ƙona akwai mutum 11 da suka fito daga mazaɓun yankin sa na Kibiya da Bunkure, inda wasu 6 suka samu muggan raunuka suna karɓar Magani yanzu haka a jihar Edo.
A cewar Ɗan Majalisar, “Wannan abu da matasan garin Uromi a jihar Edo, suka yi ya saɓa da dokar kasa, kuma mummunan laifi ne, a don haka za mu bi kadin hakƙin mutanen mu da aka kashe a kuma waɗanda aka jikkata, “in ji shi“.
Kabiru Rurum, ya ce a matsayinsa na wakilin mutanen da aka kashe a majalisar Wakilai ta ƙasa, yana kira ga shugaban Najeriya Bola Tinubu, da babban Sifeton ƴan sanda, da su yi duk mai yiyuwa wajen ganin an kamo waɗanda suka yi wannan aika-aikar tare da hukunta su, da kuma biyan diyya ga iyalan waɗanda suka rasu da kula da waɗanda suka jikkata.
“Kasancewar wannan bashi ne na farko da ake samun wasu ɓata gari na tare matafiya akan hanya da basu ji ba basu gani ba su kashe su, a don haka muna fatan wannan karon gwamnati da sauran hukumomin tsaro za su ƙaddamar da ƙwaƙƙwaran bincike don ɗaukae mataki kamar yadda dokar kasa ta tanada, “in ji Rurum”.
Ɗan majalisar ya kuma jajantawa dukkanin al’ummar jihar Kano musamman Iyalan waɗanda suka rasu, tare da addu’ar Allah ya gafarta musu yasa Jannatul Firdausi makomar su, su kuma waɗanda suka jikkata Allah ya basu lafiya.
-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai4 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi5 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su