Wasanni
Chelsea ta gaggauta daukar Osimhen bayan sun dauki Nkunku – Burley

Tsohon Shahararren dan wasan Chelsea, Craig Burley y ana son kungiyar ta dauko Victor Osimhen, bayan sun kammala cinikin Christopher Nkunku.
A na sa ran Nkunku zai kulla yarjejeniya da kungiyar West London a bazara mai zuwa, bayan kungiyarsa ta Bundesliga, RB Leipzig da Chelsea sun amince kan cinikin.
Osimhen dai ya haskaka a gasar Seria A bana kuma ana alakanta shi da komawa Chelsea da wasu kungiyoyin Turai.
Burley ya yi imanin haduwar Osimhen da Nkunku zai yi matukar wahala ga abokan hamayya.
“Ina tsammanin shi (Nkunku) da Osimhen za su haskaka”. In ji Burley ya fada wa ESPN.
“Ban sani ba ko zai bar Napoli, amma ba za ku same shi ba sai lokacin bazara da farko.”
Osimhen ya zura kwallaye tara kuma ya taimaka aka zura kwallaye uku a wasanni 14 da ya buga a dukkanin gasa na Partenopei a kakar wasa ta bana.
Ya danganta da Napoli daga kungiyar Ligue 1, Lille a cikin 2020

Labarai
Real Madrid ta kaddamar da Alexander

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta ƙaddamar da ɗan wasa Trent Alexander Arnold a yau a matsayin ɗan wasan ta
Inda shugaban ƙungiyar Flerontino Perez yace yau suna matuƙar Farin ciki kasancewar sun mallaki babban ɗan wasan baya a duniya.
Shima ɗan Wasa Arnold ya bayyana cewa yana cikin farin ciki kuma mafarkin sa ya cika na zama ɗan Wasan Madrid a yau.

Labarai
Arsenal ba kanwar lasa ba ce – Me tsaron Gidan Real Madrid

Me tsaron Gidan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Thibaut Courtois yace sun yi rashin nasara ne a wasan da suka buga a jiya da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, saboda Arsenal din ba kanwar lasa ba ce.
A jiya Laraba ne dai aka fafata wasan kusa da na kusa da na karshe, tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da kuma Arsenal Inda Arsenal ta lallasa Real Madrid da ci 2 da 1.

Wasanni
Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta 2023/2024.

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta shekarar 2023/2024, bayan da suka samu nasara a kan Weder Bremen da ci 5-0.
Hakan ne kuma ya kawo ƙarshen shekaru 11 da Bayern Munich, da ta yi tana lashe gasar.
Wannan dai shi ne karo na farko da Bayer Leverkusen suka taɓa lashe gasar a tarihi, ida suka gaza ɗaukar kofin a shekarar 2002 a ranar ƙarshe ta gasar.
Har ila yau, a dai wannan shekarar ne su kayi rashin nasara hannun Shalke 04, a wasan ƙarshe na German Cup Da ci 4-2.
Haka kuma, Real Madrid suka doke su a wasan ƙarshe na zakarun nahiyar turai.
Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar bata taɓa ɗaukar wata gasa ba a ƙarni na 21, sai bayan da Xavi Alonso ya karɓe su.

-
Nishadi6 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai5 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi6 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi6 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su