Connect with us

Manyan Labarai

Gwamnati za ta samar da jami’an tsaro na musamman domin kula da sufurin jiragen kasa

Published

on

Gwamnatin tarayya tace za ta samar da jami’an tsaro na musamman da za su rinƙa kula da sufurin jiragen ƙasa a wani ɓangare na matakan magance hare-haren da ake kai wa jiragen da fasinjoji a ƙasar.

Ƙaramin ministan sufuri na ƙasar Ademola Adegoroye ne ya bayyana haka lokacin da ya kai ziyara tashar jirgin ƙasa ta Tom Ikimi a ƙaramar hukumar Igueben da ke jihar Edo, wadda ‘yan bindiga suka kai wa hari a ƙarshen makon da ya gabata tare da yin garkuwa da fasinjoji.

A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar sufurin ƙasar nan ya fitar, ya ce gwamnatin za ta ɗauki matakan da suka dace domin magance matsalar hare-hare kan tasoshin jiragen ƙasa domin tabbatar da kariya ga fasinjoji da kayayyakin aikin hukumar.

Daga cikin matakan da ya ce hukumar za ta ɗauka har da haɗa kai tsakanin hukumar da al’umma mazauna yankunan da tasoshin jiragen suke domin samar da tsaro da tashoshin jiragen.

Haka kuma ministan ya yi watsi da fargabar da ake yi na cewa gwamnati za ta rufe zirga-zirgar jiragen ƙasa a faɗin ƙasar nan, yana mai cewa gwamnatin tarayya da hukumar sufurin jiragen ƙasa ba su da wannan niyya, sannan kuma za a ci-gaba da sufurin.

Hangen Dala

Zargin Almundahana:- An kama jami’in gwamnatin Kano

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tabbatar da kama Tasiu Al’amin-Roba, babban mataimaki na musamman (SSA), ga gwamnan jihar kano da kuma wani Abdulkadir Muhammad bisa zargin su da karkatar da kayan abincin tallafi a jihar Kano.

 

Kwamishinan ‘yan sandan, Hussaini Gumel, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN hakan a wata hira ta wayar tarho a ranar Lahadi cewa, an kama wadanda ake zargin ne a wani dakin ajiyar kaya da ke Sharada dauke da jakunkuna sama da 200.

 

Ya kara da cewa wadanda ake zargin sun yi awon gaba da shinkafa da masara a ma’ajiyar da ke Sharada.

 

“Tun daga lokacin ne muka fara bincike mai zurfi don gano buhunan masara ko shinkafa nawa aka diba aka sayar da su,” inji shi.

 

Gumel ya ce za a gurfanar da mutanen biyu a gaban kotu bayan kammala bincike .

Continue Reading

Hangen Dala

An yiwa kasafin Kudin 2024 karatu na biyu

Published

on

Majalisar Dattawan Najeriya da ta Wakilai sun yi wa kasafin kuɗin ƙasar na 2024 karatu na biyu ranar Juma’a kwana biyu bayan Shugaba Bola Tinubu ya gabatar musu da shi.

A ranar Laraba ne Tinubu ya je majalisar tare da gabatar da naira tiriliyan 27.5 a matsayin kasafin abin da gwamnatinsa za ta kashe a 2024, kuma ya nemi ‘yan majalisar su gaggauta amincewa da shi.

Sai dai shugaban bai bayyana adadin abin da kowace ma’aikata da hukumomin gwamnati za su samu ba a lokacin da ya yi gabatarwar, abin da ya jawo cecekuce da muhawara a ƙasar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito ‘yan majalisar na kokawa yayin muhawarar da suka yi ranar Juma’a game da ƙarancin bayanai kan kasafin, wanda suka ce ya sa sun mayar da hankali ne kawai kan abubuwan da Tinubu ya faɗa a jawabinsa.

Jam’iyyun adawa sun soki kasafin da cewa “na yaudara ne”, yayin da Shugaba Tinubu ya yi masa laƙabi da “kasafin sabunta fata”.

Continue Reading

Manyan Labarai

Hajiya Aisha Bura ta lashe zaben shugaban mata yan jarida na kasa NAWOJ

Published

on

Zaɓaɓɓiyar shugabar kungiyar mata ƴan jarida ta ƙasa Hajiya Aisha Ibrahim Bura ta alkawarta yin tafiya da kowanne bangare domin samar da hadin kai da ci gaban mambobin kungiyar.

Hajiya Aisha Bura ta bayyana hakan jim kadan bayan kammala rantsar da ita a matsayin wadda ta samu nasarar lashe zaben da aka gudanar a daren jiya.

Ta ce, akwai bukatar mambobin kungiyar su bata hadin kai don ganin ta sauke nauyin da ya rataya a wuyanta.

Hajiya Aisha Ibrahim Bura ta samu nasara da kuri’u 498 yayin da abokiyar takarar ta kuma shugabar kungiyar mai barin gado Hajiya Ladi Bala ta samu kuri’u 381.


Continue Reading

Trending