Connect with us

Hangen Dala

Kotun koli:- Lauyoyi 200 zasu taimakawa Abba Gida Gida

Published

on

Ayarin wasu lauyoyi har sama da 200 daga jihohin arewacin Nigeria 19, sun gargadi Shugaban kasa Bola Tinubu da kotun ƙolin Nigeria game da Shari’ar gwamnan jihar kano dake gaban kotun ƙoli a halin yanzu.

 

Mun damu kawai da gaske dangane da abin da ya faru a Kotun daukaka kara na hukuncin da ta yanke na zaben gwamnan jihar Kano a 2023, inda suka dage cewa dole ne a bi doka don tabbatar da kuri’un kowane dan Najeriya a lokacin zabe”.

 

Da yake magana a madadin lauyoyin da ke karkashin tutar Abba Kabir Yusuf Volunteer Lawyers Forum For The 19 – Northern Jihohin da kuma Abuja a wani taron manema labarai da suka gudanar a Arewa House Kaduna ranar Lahadi, Barista Yusuf Ado Ibrahim ya bayyana cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da kotun koli bai kamata a bar Najeriya ta zama kasar jam’iyya daya ba domin hakan ya sabawa ka’idojin dimokuradiyya .

 

“A tarihi, idan aka yi la’akari da tsohuwar Nijeriya, shugabanninmu na baya irin su Sir Ahmadu Bello masu albarka da sauran su a kodayaushe suna mutunta doka da tsarin dimokuradiyya, a don hakaka ne muke kira ga shugaban mu, Bola Ahmed Tinubu da bangaren shari’a su mutunta doka kuma su bijirewa yunkurin gudanar da tsarin jam’iyya daya a Nijeriya, tare da ba da tabbacin kuri’un duk wani mai zabe a Nigeria sun yi amfani a lokaci zabe kamar yadda kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999 ya tanada.

 

Zargin Almundahana: Yan sanda sun kama wani hadimin gwamnan Kano

 

Wannan ba ya rasa nasaba da yadda mutanen Kano nsuka kada kuri’ar goyon bayan gwamna Abba Kabir Yusuf domin ba shi damar ci gaba da ayyukan alherin da zasu kara inganta rayuwar al’ummar jihar Kano,” inji kungiyar.

 

Kungiyar a wajen taron, ta kuma bukaci a sake fasalin dokar zabe.

 

“Yana da kyau a bayyana a nan cewa dokar zabe na bukatar sake yi mata gyare-gyare domin magance wadannan matsalolin da suka shafi tsarin shari’a da dimokuradiyya, ya kamata a ce ana gama duk harkokin Shari’ar Zaɓe kafin rantsar da wadanda suka lashe zaben don gudun sake faruwar irin Wadannan abubuwan.

 

Batutuwan sun yi yawa da ba za a iya ambata ba. Amma dukkanmu muna zaune a nan mun yi imani da karfi na tsarin shari’a mai ‘yanci. Mun yarda da gazawar alkalan mu a matsayinmu na mutane, muna fatan kotun koli za ta yi abin da ya dace wajen yanke hukunci ba tare da kokarin dadadawa wani ko wasu ba”.

 

“Muna fatan cewa za a kare martabar talakawan jihar Kano tare da mutunta zabinsu, muna kuma da yakinin cewa Kotun Koli za ta yi adalci ta hanyar tabbatar da bayyana cewa zababben Gwamnan Jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf, wanda jama’ar jihar Kano shi ne yayi nasara.

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Hangen Dala

Gaya Ajingi Albasu:- Dan majalisa ya raba kayan abinci

Published

on

Dan majalisar Tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Gaya, Ajingi da Albasu Dakta Ghali Mustafa Fanda ya fara rabon tallafin kayan abinci ga al’ummar kananan hukumomin uku.

 

Yayin rabon tallafin kayan abincin, Dakta Ghali Mustafa yace yayi rabon tallafin ne domin fara sauke nauyin al’ummar da yake wakilta.

 

” Wannan tallafi zamu bayar da shi ne domin fara sauke nauyin al’ummar da suka zabe mu, kuma wannan shi ne karon farko, kuma yayi daidai da bukatar al’umma a yanzu, shiyasa muka fara da tallafin kayan abinci”.

 

“A cikin wannan tallafi mutane kimanin dubu ashirin ne zasu amfana, wanda zamu bayar da buhunan Shinkafa da Gero da Garin masara.”

 

Haka kuma ɗan majalisar ya bayar da tallafin Naira miliyan ashirin ga matasan kananan hukumomin Gaya, Ajingi da Albasu.

 

Sai kuma ɓangaren dalibai mata, wanda shima a yau dan majalisar ya dauki nauyin karatun dalibai mata guda 60 a bangaren lafiya.

 

Haka kuma cikin jawabin nasa Hon Ghali ya kuma ce nan gaba kadan zai bayar da tallafin taki ga manoma, da kuma farfaɗo da dukkanin rijiyon burtsatse na kananan hukumomin Gaya, Ajingi da Albasu a wani mataki na samar da ruwan sha.

 

Da yake nasa jawabin mataimakin gwamnan Kano Kwamred Aminu Abdussalam Gwarzo wanda ya samu wakilcin mai baiwa Gwamna Shawara kan harkokin siyasa Hon Sunusi Surajo Kwankwaso kira yayi ga sauran wakilan al’umma da suyi koyi da Dakta Ghali Mustafa Fanda wajen ayyukan alkhairi da kuma jin kan al’umma.

 

Haka kuma Hon Sunusi Surajo ya yabawa dan majalisar bisa bayar da tallafin ga ƙananan hukumomin uku.

 

Taron dai wanda ya gudana a cikin Islamic Centre na karamar hukumar Gaya ya samu halartar manya, da kuma jagororin yankunan uku, kuma nan take Dan majalisar Tarayya Dakta Ghali Mustafa ya fara rabon tallafin

Continue Reading

Hangen Dala

Shugaban kasa ya bayar da umarnin bude Boda

Published

on

Shugaban kasa Asuwaju Bola Ahmad Tinubu ya bayar da umarnin bude iyakokin kasar nan.

Cikin sanarwar da ya fitar shugaban ya ce duk wata iyaka dake tsakanin Nigeria da jamhuriyar Nijar a gaggauta bude ta.

Karin bayani na nan tafe…

Continue Reading

Trending