Connect with us

Addini

Kuyi hakuri idan aka yi muku kazafin wani abu – Limamin Masallacin Madina

Published

on

Limamin Masallacin Juma’a na Madina Sheikh Abdulmuhsin Bin Muhammad Alkasim, ya ce babu abu mafi muni dake saurin jefa wanda ya aikatashi a cikin wutar jahannama sama da yin kazafi.

Sheikh Abdulmuhsin bin Muhammad, ya bayyana hakan ne ta cikin hudubar juma’ar da ya gabatar yau a masallacin, wanda Dakta Maryam Abubakar Abba ta fassara ta cikin shirin Rauda Min Riyadil Janna na nan gidan rediyon Dala FM Kano, da ya gudana a safiyar Juma’ar nan.

Sheikh Abdulmuhsin ya kuma kara da cewa babu wadanda akafi jarrabawa sama da Annabawa, da kuma mumunai, kamar yadda aka jarrabi nana Aisha Uwar Mumunai, kuma da suka yi hakuri suka cinye jarabawar.

Wakilinmu Nasir Khalid Abubakar ya rawaito cewa Sheikh Abdulmuhsin ya kuma ja janhankali ga duk mutumin da aka jarraba da kazafi, da ya yi hakuri har Allah S.W.T, ya wankeshi daga wannan kazafin, kamar yadda Ubangiji ya wanke Nana A’isha Allah ya kara mata yadda.

Addini

Hajji2025: Maniyyatan Najeriya 16,182, sun sauka a Saudiyya – NAHCON

Published

on

Hukumar kula da Alhazai ta Najeriya, NAHCON, ta ce izuwa yanzu aƙalla maniyyatan ƙasar su 16,182, ne suka sauka a ƙasar Saudiyya, domin gudanar da aikin Hajjin bana na shekarar 2025.

Hukumar ta NAHCON, ta bayyana hakan ne da yammacin Alhamis ɗin nan a shafinta na Facebook, ta ce aƙalla jirage 40, ne suka yi jigilar maniyyatan, daga ranar juma’ar da ta gabata, da aka fara kai maniyyatan zuwa ƙasa mai tsarki.

 

NAHCON, ta ƙara da cewa, jirgi na ƙarshe da ya sauka a Madinah, shi ne jirgin UMZA, mai lamba UMZ3412, da ya tashi ɗauke da maniyyatan jihar Kaduna su 299, Maza 229, mata kuma 70, sai wasu na musamman su 9.

Continue Reading

Addini

Hajjin2025: Maniyyatan Najeriya 3,644, sun sauka a Saudiyya

Published

on

Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON, ta ce zuwa yanzu Maniyyatan ƙasar nan su dubu 3,644, ne suka sauka a ƙasa mai tsarki, domin sauke Farali a aikin hajjin bana, na shekarar 2025.

Kazalika, hukumar ta ce aƙalla jirage Tara ne suka yi jigilar maniyyatan, biyo bayan saukar maniyyatan jihar Oyo su 550, Maza 302, Mata kuma 248, wanda jirgin ya sauka da misalin ƙarfe 05:54 na yammacin yau Asabar.

A ranar Juma’a 09 ga watan Mayun 2025, ne dai mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shateema, da shugaban hukumar Alhazai na ƙasa NAHCON, Farfesa Abdullahi Sale Usman, da gwamnan jihar Imo Hope Uzodinma, suka ƙaddamar da tashin Maniyyatan a birnin Owerri na jihar Imo.

Continue Reading

Addini

Harsuna 20 da za’a fassara huɗubar Arfah ta 2025, ciki har da Hausa a Saudiyya.

Published

on

Hukumar kula da aikin Hajji da Umrah ta kasar Saudiyya, ta ce za’a fassara huɗubar Arfah, ta shekarar 2025/1446, zuwa harsuna guda 20.

Shafin sada zumunta na Inside the Haramain Sharifai, ne ya wallafa hakan, yana mai cewa harsunan da za a fassara huɗubar ta Arfah, sune kamar haka.

1. Turanci
2. Faransanci
3. Malay
4. Urdu
5. Farisa/Farsi
6. Sinanci
7. Turkanci
8. Rashanci
9. Hausa
10. Bengali.

Sauran harsunan sune kamar haka.

11. Harshen mutanen Sweden
12. Harshen mutanen Espanya
13. Swahili
14. Amharic
15. Italiyanci
16. Fotigal
17. Bosniya
18. Malayalam
19. Harshen Filifino
20. Jamusanci.

Continue Reading

Trending