Connect with us

Labarai

Mun kulle Asibitoci masu zaman kan su 12 a Kano – PHIMA

Published

on

Hukumar da ke kula da Asibitoci masu zaman kan su ta jihar Kano PHIMA, ta ce zata ci gaba da daukar mataki akan dukkanin Asibitocin da suka saɓa ƙa’idar aiki, domin tsaftace harkar tare da samun damar kulawa da marasa lafiya cikin ka’ida.

Shugaban hukumar ta PHIMA, a nan Kano Farfesa Salisu Ahmad Ibrahim, ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da gidan rediyon Dala FM, a ranar Juma’a 05 ga watan Yunin 2024.

Farfesa Salisu Ahmad, ya kuma ce daga zuwan sa hukumar zuwa yanzu aƙalla sun kulle Asibitoci guda 12, kuma akwai uku daga ciki an cire su daga tsarin asibitoci gaba ɗaya bisa sablɓa ka’idar aiki.

“Zamu ɗauki mataki akan dukkanin masu magungunan gargajiyar da suke zagayawa cikin unguwanni suna damun mutane da karar amsa kuwa, ko kuma bayyana batsa ta hanyar tallata magungunan nasu, domin tsaftace harkar, in ji Salisu”.

Wakilinmu Abdulkadir Muhammad Sani Tukuntawa ya rawaito cewa Farfesa Salisu Ahmad Ibrahim, ya kara da cewa yanzu haka hukumar ta PHIMA, tayi nisa wajen yiwa masu magungunan gargajiya
rijista tare da tantance su, domin tsarkake harkar da kuma gujewa fuskantar matsala.

Hangen Dala

Rashin wuta: Muna cikin mawuyacin hali – al’ummar Kano, Katsina da Jigawa

Published

on

Al’ummar jihohin Kano, katsina da Jigawa na fuskantar yanayi mara dadi, Sakamakon karancin samun wutar lantarki daga hukumar KEDCO.

Al’ummar jihohin sun ce iya sa’o’i uku kacal suke samun wutar, wanda hakan ke haifar musu da nakasu a harkokin kasuwancin su.

Wani bincike da jaridar Daily Trust tayi ta ambato yadda masu kananan masana’antu irin su Walda, Cajin Waya, Kankara da masu sana’ar dinki da dai sauran kananan sana’o’i dake amfani da wutar lantarki sun shiga mawuyacin hali.

Kazalika rashin wutar ya shafi hatta bangaren ruwan sha, dama masu sana’ar sayar da Ruwa a irin yankunan Hotoro da sauran irin wuraren dake sayen ruwa, Inda yanzu haka ruwan yayi tashin gwauron zabi a kowace jarka.

Koda dai ana ta bangaren hukumar rarraba hasken wutar lantarkin me kula da shiyyar Kano, Katsina da Jigawa KEDCO sun nemi afuwar al’umma.

Idan za’a tuna dai a makon jiya ne Ministan Wutar lantarki yace ‘yan Nigeria Miliyan 150 na samun wadatacciyar wutar lantarki.

Sai dai kuma a jihohi irin su Kano, Katsina da Jigawa na bayyana damuwa kan karancin Wutar, Inda suka ce bata wuce ta sa’o’i uku suke samu a kowa ce rana.

Continue Reading

Hangen Dala

Rashin wuta:- Muna cikin mawuyacin hali – al’ummar Kano, Katsina da Jigawa

Ci gaba ba ya zuwa sai an samu haɗin kan al’umma – Dagacin Ja’en

Published

on

Dagacin garin Ja’en da ke ƙaramar hukumar Gwale a jihar Kano, Alhaji Isma’il Sa’ad Usman, ya ce hadin kai ne kaɗai zai kawo ci gaba ga kowa ce irin al’umma.

Dagacin ya bayyana hakan ne Jim kaɗan bayan wani taron masu Ruwa da tsaki na Garin Ja’en, wanda Hakimin Gundumar Ɗorayi Barde Kerarriya Alhaji Shehu Kabir Bayero ya shirya, aka gudanar a yankin Ja’en a ƙarshen makon da ya gabata.

“Dukkanin wani ci gaba ba ya zuwa har sai an samu haɗin kan kowa ne bangare na al’umma, “in ji Dagacin”.

Wakilin Dala FM Kano, Ahmad Rabi’u Ja’en ya ruwaito cewa, taron ya samu halartar dukkanin bangarori, na unguwannin Ja’en, da suka haɗar da kungiyar mafarauta da maharba dabma kungiyar malaman makaranta.

Continue Reading

Trending