Connect with us

Labarai

Mun cafke matashin da ke dillancin ƙwayoyi a Kano – Rundunar Anti-Snaching Phone

Published

on

Rundunar tsaro da ke yaƙi da ƙwacen waya da faɗan Daba da kuma kawar da Shaye-shaye ta Anti Snaching Phone da ke jihar Kano, ta samu nasarar cafke wani Matashi bisa zargin sa da dillancin ƙwayoyi da suke sanya maye, tare da tinzira masu sha suna yin abubuwan da suka saɓawa hankali.

Matashin mai suna Markus Danladi mazaunin unguwar Rinji, dan asalin jihar Adamawa, an zargeshi ne da cewar, yana sayar da sayar wa mutane musamman ma Matasa ƙwayoyi a unguwar Ja’en layin Salasa da ke ƙaramar hukumar Gwale.

Ƙwayoyin da ake zargin matashin yana sayarwa sun tasamma guda ɗari tara, waɗanda suke sanya maye tare da fitar da mutum daga cikin gayyacin sa idan ya sha.

Bayan kama matashi Markus Ɗanladi da tarin ƙwayoyin ya shaidawa Dala FM Kano cewar, yana sayar wa mutane musamman ma Matasa ƙwayoyin ne a yankin Ja’en, amma ya yi nadama ba zai ƙara ba idan aka sake shi, saboda babu riba a cikin harkar.

Matashin ya ƙara da cewa a shirye yake wajen ganin ya gyara halin sa, domin kuwa ya yi ritaya a harkokin dillancin kwayoyin da yake yi tun da babu riba a ciki.

Da yake jawabi kwamandan rundunar tsaron da ke yaƙi da masu kwacen waya da kawar da Shaye-shaye da kuma magance fadan Daba ta Anti Snaching Phone ta jihar Kano, Inuwa Salisu Sharaɗa, ya ce sun cafke matashin ne a ƙoƙarin su na magance harkokin sha da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi a jihar Kano.

Ya kuma ce da zarar sun kammala bincike za su gurfanar dashi a gaban kotu, domin girbar abinda ya shuka, yana mai cewa za su faɗaɗa aikace-aikacen su domin kakkaɓe ɓata garin da ke damun al’umma a sassan jihar Kano.

Baba Suda

Hukumar tattara kudaden shiga ta Kano ta rufe wasu bankuna

Published

on

Hukumar Tattara kudaden shiga ta jahar kano ta kulle bakin Eco da Zenith dake kan titin Murtala Muhammad. Sakamakon rashin biyan haraji.

Cikakken labarin na Zuwa….

Continue Reading

Baba Suda

Kisan Makurdi:- Gwamnatin Kano za ta tura wakilai

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano tayi Allah wadai da kisan mutane biyu Yan Jihar a garin Makurdi dake Jihar Benue.

Cikin sanarwar da Daraktan Gwamnan Kano kan harkokin yada labarai Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ta ruwaito Gwamnan na Mika sakon jaje ga alummar Jihar da iyalai da ‘yan uwan wadanda abin ya rutsa dasu, Barhma Suleman da Jamilu Ahmad.

 

Kazalika Gwamnan yayi alkawarin daukar Matakin da ya dace kan batun, tare da fadin gwamnatin Kano za ta tashi wakilai har Zuwa Jihar Benue domin tabbatar da daukar Matakin da ya dace.

 

 

Continue Reading

Baba Suda

NNPP:- Kwankwaso ya sulhunta rikicin jamiyyar

Published

on

Rahotanni daga Abuja sun tabbatar da jagoran kwankwasiyya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi wani zama da Dan majalisar tarayya Mai wakiltar kananan hukumomin Rimin Gado, Tofa da Dawakin Tofa, Wato Honorable Abdulkadir Jobe, da kuma Daraktan yada labaran Gwamnan Kano Honorable Sunusi Bature Dawakin Tofa.

 

Ganawar wadda ta gudana a yammacin wannan Alhamis ta kawo karshen Jan Zaren dake faruwa tsakanin Dan majalisar da kuma Sunusi Bature.

 

A baya bayan nan dai an kai ruwa rana tsakanin su, Inda kowa ne bangare ke mayar da martani.

Abdulkadir Jobe da kuma Sunusi Bature dukkanin su mabiya jamiyyar NNPP ne tsagin kwankwasiyya.

Continue Reading

Trending