Connect with us

Manyan Labarai

Daba a Kano: Mun kama matasa 51 a cikin kwanaki uku – Ƴan Sanda

Published

on

A ƙoƙarin ta na magance harkokin faɗan Daba da fashin Waya, rundunar Ƴan Sandan jihar Kano, ta kama Matasa 51, cikin kwanaki uku a birnin jihar, tare da samun da muggan Makamai da kuma kayan maye.

A cikin sanarwar da mataimakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar DSP Hussain Abdullahi, ya fitar a cikin daren Litinin, ta ce an kama matasan ne a ƙananan hukumomin ƙwaryar birnin Kano, irin su Tarauni, da Gwale, da Dala, Kano Municipal, a cikin unguwannin Zage, Ƙofar Mata, Kurna, da Rijiyar Lemo, Hotoro, da Sheka.

Rundunar ƴan sandan ta kuma ce ba za ta lamunci yadda wasu matasa ke amfani da makamai yayin kiɗan Gangi, lamarin da a wasu lokutan ake ɗaukar su a bidiyo, ko Hotuna riƙe da makamai ana yaɗawa a shafukan Tik-Tok, Facebook, X, da Instagram, da sauran su, abinda ke ƙarawa masu faɗan daban ƙwarin gwiwa akan lamarin.

Cikin sanarwar, Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano Ibrahim Adamu Bakori, ya kuma buƙaci iyaye da su ƙara bibiyar al’amuran ƴaƴan su, tare da ɗaukar matakan da suka dace da zarar sun ga halayyar ƴaƴan nasu ta fara canzawa.

A cewar sanarwar, duk wanda ya ga faruwar wani abu da ka iya kawo matsalar tsaro zai iya kiran waɗannan lambobin wayar domin bada bayanan sirri, akan 08032600299, ko 08032600300, ko kuma 08032600301.

Rundunar ta kuma nuna jin daɗin ta bisa haɗin kan da take samu daga ɓangaren al’umma, a ƙoƙarin su na tabbatar da tsaro da zaman lafiya a faɗin jihar Kano.

Kwamishinan ƴan sandan na jihar Kano Ibrahim Bakori, ya kuma bada umarnin fara wasu ayyuka na ba sani ba sabo, amma fa sai an ɗauka da Hakuri, da ƴan daban, da kuma iyayen da suka bar Makami a Gidansu.

Tashar Dala FM Kano ta ruwaito cewa, ko a ranar Asabar dai, sai da Kwamishian ƴan sandan Kano ta ƙaddamar da sabbin dabarun daƙile harkokin faɗan Daba da fashin Waya da Makami, da sauran ayyuka, a jihar, bayan ganawar sa da manyan jami’an tsaro.

Manyan Labarai

Da Ɗumi-ɗumi: An sallami Ɗan Bello bayan kama shi da aka yi a Kano

Published

on

Rahotanni sun bayyana cewa ƴan mintuna kaɗan da tsare Bello Habib Galadanci da aka fi sani da Ɗan Bello, yanzu haka an sallame shi ba tare da ɓata lokaci ba.

Majiyoyin dai sun bayyana cewa jami’an tsaro ne da ake zargin daga Abuja suke suka kama matashi Bello Habib Galadanci da aka fi sani da Ɗan Bello, a ranar Asabar 12 ga watan Yulin 2025.

Rahotannin sun bayyana cewa an kama Ɗan Bello, ne a filin jirgin saman Malam Aminu Kano, a ranar Asabar 12 ga watan Yulin 2025, kamar yadda DW Hausa ta ruwaito.

Sai dai kawo lokacin da muke kammala haɗa wannan labarin jami’an tsaron ba su fitar da wata sanarwar akan lamarin ba, amma hakan akan ne muka yi ƙoƙarin ji daga ɓangaren kakakin rundunar ƴan sandan Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ta wayar tarho, sai dai kawo yanzu haƙan mu bata cimma ruwa ba.

Tuni dai kama Ɗan Bello ya fara janyo cece-kuce a tsakanin al’umma, musamman ma da wasu ke alaƙanta kama shi da zanga-zangar da suka shirya gudanarwa a ranar 21 ga wannan wata na Yulin 2025, akan nuna damuwa kan tsarin bada fansho ga tsofaffin ƴan sanda a Najeriya.

Continue Reading

Manyan Labarai

Ku fito sallar roƙon ruwan da za mu gudanar a Kano don neman ruwan sama – Majalisar Malamai

Published

on

Majalisar malamai ta jihar Kano ta buƙaci al’umma da su fito sallar roƙon ruwa da za ta jagoranta a gobe Asabar, domin neman dacewa da samun ruwan duba da yadda ake ci gaba da fuskantar ƙarancinsa, ga kuma Damuna na ƙara yin nisa.

A cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun shugaban majalisar malaman ta jihar Kano Mallam Ibrahim Khalil, ta ce za a gudanar da sallar roƙon ruwan ne tare da addu’o’i, a masallacin Umar Bin Khattab da ke Dangi kan titin Zaria a Kano.

Sanarwar ta kuma buƙaci dukkanin al’umma da su fito sallar roƙon ruwan domin neman taimakon Allah madaukakin Sarki, wajen samun ruwan, bisa ƙarancin ruwa da ake fama da shi duk kuwa da Damina na ci gaba da nisa.

 

Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da al’umma ciki har da Manoma ke ci gaba da addu’a kan Allah ya saukar musu da ruwan sama mai albarka, bisa yadda ake ci gaba da fuskantar ƙarancin sa a halin yanzu.

Continue Reading

Manyan Labarai

Wasu lauyoyin gwamnatin Kano sun shirya shiga yajin aiki matuƙar kwamishinan Shari’a bai daina yi musu katsalandan ba.

Published

on

Wasu lauyoyin gwamnatin Kano da suka roki a sakaya sunansu, sun yi barazanar tsunduma yajin aiki, bisa yadda suka zargi kwamishinan shari’a na jihar Kano Barista Isah Haruna Dederi, yana mayar musu da aiki baya.

Lauyoyin sun bayyana fushin su ne akan cewar kwamishinan Shari’a na jihar kano da zargin ya hana su haƙƙoƙinsu na hular gashin doki da rigar zuwa kotu da kuma na’ura mai ƙwaƙwalwa wadda gwamnan Kano ya bayar da umarnin a basu, lamarin kawo yanzu ya gagara.

Kaza lika, luyoyin sun bayyana irin cin dunduniyar da ake yi wa aikinsu da zarar an kawo takardun tuhuma akan zargin fyade ko kuma kisan kai, ko fashi da makami inda suka ce suna kammala bincike idan sun samu mutum da laifi a wasu lokutan sai kwamishin ya yi umarnin a saki mutumin da ake zargin maimakon a kai shi kotun da ta ke da hurumin yi masa Shari’a.

Akan wannan zarge-zargen kwamishinan ta bakin babban sakatare a ma’aikatar Shari’a Barrister Mustafa Muhammad Nuraddin ya musanta wannan zarge-zarge, al’amarin da ya ce bashi da tushe ballantana makama.

Ma’aikatar Shari’a dai nan ce ake gudanar da bincike akan manyan laifuka da zarar yansanda sun kammala nasu binciken, domin yin abinda ya dace.

Continue Reading

Trending